Najeriya ta samu sabbin taragon jirgin kasa na zamani guda 10 – Minista

Najeriya ta samu sabbin taragon jirgin kasa na zamani guda 10 – Minista

Akalla sabbin taraggan jirgin kasa guda goma ne zasu shigo Najeriya daga kasar China a watan Yuni mai zuwa don kara adadin taraggan jirgin kasan dake sakarar jama’a da kayansu daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasar China ce ta kera ma Najeriya taraggan jirgin kasa guda sittin da hudu (64), daga ciki ne guda goma zasu shigo Najeriya a watan Yuni don amfani dasu a layin dogon Kaduna zuwa Abuja, yayin da sauran 54 zasu aiki a layin dogon Lagos - Ibadan da Warri – Itakpe.

KU KARANTA: A rina: Ana biyan Sojan Najeriya N1000, ana biyan dan Boko Haram $3000 a duk rana

Minista Amaechi ya tabbatar da haka ne a yayin wata ziyarar daya kai kasar China a karshen makon data gabata don game ma kansa aikin kera taraggan jirgin, wanda gwamnati ta baiwa kamfanin Chines Railway Rolling Stocl Corporation, CRRC, kwangila.

“Muna bukatar sabbin taraggan nan zuwa Yuni, muna bukatar taraggan saboda daukan jama’a daga wuri zuwa wuri, kuma akalla guda goma muke nema a yanzu saboda muna bukatar inganta aikin jirgin kasa dake safara daga Kaduna zuwa Abuja.” Inji shi.

Sai dai Minista Amaechi ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda aikin kera taraggan ke tafiyar hawainiya, don haka ya nemi kamfanin CRRC su kara zage damtse su tabbatar da kammala aikin a lokacin da aka diban mata, a cewarsa sun ma wuce lokacin da aka shirya dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel