Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya sun ragargarji yan Boko Haram a Damaturu da daren nan (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya sun ragargarji yan Boko Haram a Damaturu da daren nan (Hotuna)

Dakarun rundunar sojin 233 Batallion na hukumar sojin Najeriya sun ragargaji wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram da suka kawo hari Damaturu, babban birnin jihar Yobe da yammacin Talata, 9 ga watan Afrilu, 2019.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita inda tace: "Jaruman sojin 233 Bataliya a yau 9 ga Afrilu 2019 misalin karfe 6 na yamma sun kawar da yan Boko Haram da sukayi kokarin shiga Damaturu, birnin jihar Yobe ta hanyar Kukareta."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi magana kan kashe-kashen jihar Kaduna

Mun kawo rahoton cewa babbar birnin jihar Yobe, Damaturu, na karkashin harin Boko Haram a yanzu haka. Mazauna yankin maisandari, wajen Damaturu sunce maharan sun zo ne ta yankin kudancin harin sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

Daya daga cikinsu, Usaini Maisandari, ya bayyana cewa suna a wajen gidansu lokacin da suka gano yan ta'addan na zuwa yankin cikin motoci kirar hilux.

"Dukkaninmu mun tsere don tsira. kuna jin karar harbin bindiga da na bama-bamai? Ina so kuyi mana addu'a dan Allah," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel