Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano

Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano

Kasuwar masu sana’ar sayar da kankara da ruwan sanyi na leda ta bude a jahar Kano, inda a yanzu haka suke samun gwaggwabar ciniki a dalilin tsananin yanayin zafi da ake fama dashi a wannan lokaci a Kano, dam kusan duk fadin Najeriya gaba daya.

Majiyar Legit.ng ta tattauna da wasu daga cikinsu a ranar Talata, inda suka ce suna samu ciniki yadda ya kamata tun bayan shigowar lokacin zafi kimanin wata guda daya daya gabata, inda suka ce yanayin zafin yasa matasa da dama sun fada harkar sayar da ruwa da kankara.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ya garzaya jahar Zamfara don ganin wainar da ake toyawa

Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano

Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano
Source: UGC

Wata mata dake sana’ar sayar da ruwa unguwar Sabon gari, Susan Eze ta bayyana cewa akwai riba sosai a cikin harkar, kuma yana kawo mata kudi a wannan lokaci, musamman idan aka duba da cewa mutane na yawan shan ruwa sosai a lokacin zafi.

Susan tace baya da ruwan sanyi da jama’a ke yawan bukata, haka zalika suna hadawa da neman kayan zaki irin na kwalba ko na gwangwani, da ire irensu kunun aya, kunun zaki, zobo da ma ginger, wanda take sayarwa akan N40 ko N50.

Shima wani babban dila a harkar sayar da ruwan leda a Kano, Christopher Ugbondo ya bayyana cewa shekaru takwas kenan yana wannan sana’a, kuma ya mallaki manyan dakunan ajiye kayan sanyi guda shida, inda yace yana samun ribar N10,000 a duk rana.

Haka zalika wani mai sana’ar sayar da ruwan mai suna Yahaya Bello ya bayyana cewa “A rana ina sanar da kura biyu na ruwan leda, ina samun riban naira dubu biyar (5,000) a kowanne rana.”

Ana iya gane yadda jama’a manya da yara suka rungumi sana’ar sayar da ruwan sanyi a Kano idan aka lura da yadda suka mamaye duk wata danja danja da mahadar titi, lungu lungu a da sako sako suna tallar ruwan sanyi don kauce ma zaman banza.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel