Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar

Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar

- Farfelar jirgin saman yaki mai ungulu na rundunar sojin sama tayi sanadiyar mutuwar daya daga cikin matuka jirgin

- Wanna iftila'i ya fada wa sojan da aka bayyana sunansa da cewar Umar da misalin karfe 4:00 na ranar Asabar

- Lamarin ya faru ne a garin Bama dake jihar Borno, inda sojoji ke gudanar da atisayen kakkabe mayakan kungiyar Boko Haram

Dakarun sojin sama dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Borno sun yi babban rashi bayan fankar jirginsu na yaki mai saukar ungulu tayi sanadiyar mutuwar wani babban jami'in soja mai mukamin 'air chief marsahal' da aka bayyana sunasa a matsayin Umar.

Wani daga cikin matuka jirgin da abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa jaridar TheCable cewar lamarin ya faru ne a garin Bama a yammacin ranar Asabar.

Hakan ta faru ne bayan jirgin ya samu matsala.

Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar

Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar
Source: Twitter

Marigayin, wanda ya kasance daya daga cikin matuka jirgin, ya fita ne domin dauko jakarsa, amma yayin da yake wuce wa ta jikin fankar jirgin sai ta fille masa kai, kuma nan take ya fadi matacce.

DUBA WANNAN: Na taba karbo $10m don na tabbatar ina da kudin da ake fada - Aliko Dangote

"Nan take farfelar jirgin dake aiki ta fille masa kai. Mun samu nasarar tashin jirgin, mun kuma mayar da shi sansanin mu. Babu alamar lalacewa a jikin fankar jirgin," a cewar majiyar.

Wannan iftila'i ya afka wa marigayin da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar.

Majiyar ta kara da cewa tuni aka sanar da iyalin marigayin, sannan ya kara da cewa ana shirin binne gawar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel