2019: Abba Gida-Gida ya sha alwashin karbe zaben Kano a hannun Kotu

2019: Abba Gida-Gida ya sha alwashin karbe zaben Kano a hannun Kotu

‘Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yayi wata doguwar hira da Jaridar Daily Trust a karshen makon nan inda yayi magana game da zaben da aka yi a jihar Kano.

2019: Abba Gida-Gida ya sha alwashin karbe zaben Kano a hannun Kotu
Abba Yusuf yace Kwankwaso ba yayi wa Gwamna katsalandan
Asali: Twitter

Abba K. Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana cewa Lauyoyin sa sun tattara hotuna da bidiyo da duk hujjojin da za a bukata a kotun sauraron karar zabe domin PDP ta karbo nasarar da ta samu daga hannun APC.

Injiniya Abba Yusuf ya bayyana cewa shi ne ya ci zabe amma gwamnati mai-ci ta APC tayi amfani da Jami’an tsaro da ‘Yan daba da kuma hukumar INEC wajen murde zaben cike-gibi da aka yi, amma yace gaskiya za tayi halin ta.

‘Dan takarar gwamnan a zaben na bana yake cewa Mutanen Kano da sauran duk masu lura da harkar zabe na gida da kasashen Duniya sun tabbatar da cewa ba zabe aka yi a Kano a Ranar 23 ga Watan Maris ba, don haka ya tafi kotu.

KU KARANTA: Malaman addini sun ji haushi wasu maganganun Kwankwaso

Yusuf ya kuma yi maganar alakar sa da Jagoran PDP watau Rabiu Kwankwaso wanda yace ya fi shekaru 33 yana tare da shi. Yusuf yace ya soma aiki ne da tsohon gwamnan tun su na aikin ruwa a karkashin gwamnatin jihar Kano.

Injiniyan yace bayan Kwankwaso ya zama Gwamna, ya zama masa Mai bada shawara a 1999 da 2011. Haka zalika ya zama Mai ba sa shawara a lokacin yana Minista da kuma NDDC har ta kai ya zama Kwamishina a mulkin sa biyu.

KU KARANTA: Sanatan APC ya nemi Oshiomhole yayi koyi da Shugaba Buhari

Abba Kabir Yusuf yace a lokacin da yake Kwamishina ne aka yi aikace-aikace a jihar Kano kuma yace ya fi shekara 27 da yin aure kafin ya hadu da 'Diyar yayan Kwankwaso da ya aura a matsayin matar sa ta biyu da jama'a ke ta surutu a kai.

‘Dan takarar gwamnan mai shekaru 56 a Duniya, yake cewa Matar da ya aura ta biyu ba Diyar cikin Kwankwaso bace, kuma yake cewa sun hadu ne a kasar waje ba a dalilin tsohon gwamnan ba, a lokacin yace ta rabu da Mai gidan ta na fari.

Mai neman kujerar gwamnan na Kano yace Kwankwaso ba mutum bane da zai nemi ya rika tsoma masa baki idan ya zama gwamna. Asali ma Abba Yusuf yace Sanata Kwankwaso barin jihar yake yi domin ya kyale mai mulki ya sake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel