Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na PDP ya sauya sheka

Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na PDP ya sauya sheka

- Daya daga cikin manema takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar PDP, Muhammad Sani Sidi, ya yi watsi da jam'iyyar kwanaki shida gabanin zaben gwamna

- Sidi wanda tsohon shugaban ma'aikatar NEMA, ya yi watsi da jam'iyyar PDP tare da jiga-jigai da mambobi 30,000 a jihar Kaduna

- Masu sauyin shekar kawo yanzu ba su yanke shawarar jam'iyyar da za ta tsarkake su tare da yi ma su wanka ba

Kwanaki shida gabanin gudanar zaben kujerar gwamna da ta 'yan majalisun dokoki na jihohi a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, daya daga cikin manema takarar kujerar gwamna a jam'iyyar PDP na jihar Kaduna ya yi watsi da jam'iyyar.

Muhammad Sani Sidi ya yi watsi da jam'iyyar sa ta PDP tare da jiga-jigai da mambobi 30,000 na jam'iyyar yayin da zaben gwamnan jihar ke daf da gudana inda gwamna Mallam Nasir El-Rufa'i ya kasance marikin tutar jam'iyyar APC.

Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na PDP ya sauya sheka
Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna na PDP ya sauya sheka
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, Sidi tare da mambobi da jiga-jigan jam'iyyar PDP daga kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar Kaduna sun yanke shawarar watsi da jam'iyyar da kawo yanzu ba bu shawarar komawar su wata jam'iyyar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, daya daga cikin na hannun daman Sani Sidi, Alhaji Ahmed Maiyaki, shine ya bayar da shaidar wannan lamari na guguwar sauyin sheka da ta auku cikin jihar a jam'iyyar PDP.

Sidi wanda ya kasance tsohon shugaban ma'aikatar NEMA, ya bayar da shaidar watsi da jam'iyyar PDP cikin wata rubutacciyar wasika da ya aike da ita zuwa ga shugaban jam'iyyar na mazabar sa ta Unguwan Sarki da ke karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

KARANTA KUMA: Gobara ta hallaka wani Magidanci, Mai dakinsa da 'ya'yan sa 3 a jihar Kano

Sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka yi watsi da ita sun hadar da; Peter Adada, tsohon mataimakin kakakin majalisar Kaduna, Rabi'u Bako, tsohon kwamishinan labarai na jihar kuma tsohon shugaban kananan hukumomi na jihar.

Sauran jiga-jigan da sun hadar da; Kabiru Ballah, Sani Shahada, tsohon shugaban karamar hukumar Kubau Nasiru Aliyu Damau, Aliyu Saleh Ramin Kura, Magaji Sadiq Hunkuyi, tsohon shugaban karamar hukumar Kudan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel