Rabonsa ya tsaga: Jarumin Hollywood ya tallafa ma matashi dan jahar Kaduna ta Twitter

Rabonsa ya tsaga: Jarumin Hollywood ya tallafa ma matashi dan jahar Kaduna ta Twitter

Wani fitacce kuma mashahurin mai shirya fina finai a masana’antar Fim ta kasar Amurka, Hollywood, wanda tafi duk wata masana’antar Fim girma a Duniya ya baiwa wani matashi dan asalin jahar Kaduna tallafi daga haduwarsu a shafin Twitter.

Twitter wata kafar sadarwar zamani ce dake hada daruruwan miliyoyin jama’a abota, ta wannan kafa ne Allah Ya hada jarumin Hollywood kuma bakar fata, Kevin Hart da wannan matashi mai zane zane a jahar Kaduna, Eli Waduba.

KU KARANTA: An buga an barku: Daďadďun Sanatoci 10 da zasu sake komawa majalisar dattawa

Rabonsa ya tsaga: Jarumin Hollywood ya tallafa ma matashi dan jahar Kaduna ta Twitter
Kevin
Asali: Twitter

A ranar Talata ne Waduba ya kaddamar da kokarin ganin Kevin Hart ya ga hotonsa a shafin Twitter wanda ya zana da hannunsa da Fensir, inda ya roki jama’a dasu taimaka masa wajen yayata hoton har sai Kevin Hart ya gani.

“Sunana Eli Waduba Yusuf, dan Najeriya ne ni, mazaunin Kaduna, Ina sana’ar zane zane da Fensir, kuma ina fatan kasancewa kamar @Harinzeyat. Ku taimakeni ku yayata wannan rubutun har @KevinHart4real ya gani, Nagode.” Inji shi.

Cikin awanni yan kalila aka samu ma’abota kafar sadarwar ta Twitter su 13,000 suka yayata wannan rubuta, tare da wasu 42,000 da suka nuna sha’awarsu ga wannan hoto, haka zalika yan Najeriya da dama sun yayatashi a shafukan sadarwar daban daban.

Bayan kwana daya sai maganar ta kai kunne Kevin Hart, inda bayan ya ga hoton sai yace “Na gani, kuma ina so na saya. Kuma zan tallafa maka da irin basirar da kake dashi, zan biyaka don ka zana wasu mashahuran abokaina guda uku da zan basu kyauta, aiko min da bayananka don mu fara aiki.”

Tuni dai yan Najeriya suka shiga yi masa san barka tare da yabama Kevin Hart da wannan taimaka da yayi alkawarin baiwa matashi Eli dan asalin jahar Kaduna, wannan shine rabon kwado baya hawa, ko hau kuma sai ya sauko.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel