Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya lashe kujerar Sanata

Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya lashe kujerar Sanata

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Hassan a matsayin wanda yayi nasara a zaben yan majalisa a yankin Arewa maso gabashin jihar.

Mista Hassan, wanda ya kasance dan takara a jam’iyyar APC, ya samu kuri’u 184,185 inda ya kayar da sanatan PDP mai ci, Ubale Shittu, wanda ya samu kuri’u 103,039.

Da wannan bayanin ne, jam’iyyar APC ta yi nasaran lashe zabe a dukkanin yankin Arewa maso gabashin Jigawa, wanda ke dauke da kananan hukumomi guda bakwai.

Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya lashe kujerar Sanata
Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya lashe kujerar Sanata
Asali: Depositphotos

A lokacin da yake bada sanarwar samakon zaben a cibiyar hada zabe a Hadejia, jami’in zabe Ahmed Garko, yace Mista Hassan ya ba dan adawansa Mista Shittu kashi.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 11

A halin da ake ciki, dan takaran jam’iyyar SDP, Kaugama Garba ya samu kuri’u 14,697; Ibrahim Mahmud na jam’iyyar ADC ya samu kuri’u363; Jamilu Usman na jam’iyyar DA ya samu kuri’u 218 sannan Abdullahi Muhammad na jam’iyyar PPC ya samu kuri’u 179.

Yawan kuri’u da aka kada sun kai 310,725, kimanin kiri’u 302,927 ne masu inganci sannan kuri’u 7’798 ne aka yi watsi da su a zaben. Yawan masu kada kuri’a da suka yi rijista a mazabar sun kai 576’561.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel