Jam’iyyar PRP tsaida Buhari a matsayin ‘Dan takarar ta a Jigawa

Jam’iyyar PRP tsaida Buhari a matsayin ‘Dan takarar ta a Jigawa

- Jam’iyyar PRP ta zabi ta marawa Shugaba Buhari baya a 2019

- Babbar Jam’iyyar adawar tace tayi na’am da manufofin Buhari

- Wani jigon Jam’iyyar a Yankin Jihar Jigawa ya bayyana wannan

Jam’iyyar PRP tsaida Buhari a matsayin ‘Dan takarar ta a Jigawa

‘Dan takarar SDP ya fadawa ‘Yan Jigawa su zabi APC a sama
Source: UGC

Labarin da mu ke ji yanzu shi ne, jam’iyyar adawar nan ta PRP, ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zabin ta a zaben 2019 da za ayi. Wani daga cikin manyan jam’iyyar ya bayyana wannan kwanan nan.

Yanzu dai duka-duka bai wuce kwana 2 a gudanar da zaben shugaban kasar ba inda jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa za ta goyi bayan tazarcen shugaban kasa Buhari. Ahmed Kaugama wanda yake takara a jam’iyyar ya fadi wannan.

KU KARANTA: SDP ta bayyana matsayar ta hana Donald Duke takara a kotu

Alhaji Ahmad Kaugama wanda yake neman kujerar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar hamayyar ta SDP ne ya bayyana mana wannan a wajen wani taro da aka yi. Kaugama ya nemi mutanen sa su zabi Buhari a 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, Shamsuddeen Aujara, wanda shi ne abokin takarar Ahmad Kaugama a zaben na 2019, ne ya wakilci ‘dan takarar a wajen wannan taro inda ya fadawa Mabiyan sa su zabi jam’iyyar APC a sama.

‘Dan takarar jam’iyyar dai yayi kira da Magoya bayan na sa ne su zabi Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa amma a gida kuma su zabi PRP. A baya ‘dan takarar PRP a Kano, Salihi Takai yayi irin wannan kira ga jama’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel