Bukarti ya fadawa EFCC ta ba sa sakamakon binciken fai-fen Gwamnan Kano yana karbar rashawa

Bukarti ya fadawa EFCC ta ba sa sakamakon binciken fai-fen Gwamnan Kano yana karbar rashawa

- Ana neman EFCC ta bada cikakken rahoton bidiyon da aka zargi Ganduje yana karbar rashawa

- Fitaccen Lauya Audu Bulama-Bukarti ya ba EFCC mako guda rak ta cika masa bukatun na sa

- Wannan Lauyan da ke kare hakkin jama’a yayi barazanar zuwa a kotu idan aka gaza yin haka

Bukarti ya fadawa EFCC ta ba sa sakamakon binciken fai-fen Gwamnan Kano yana karbar rashawa
Lauya ya nemi Magu ya ba sa rahoton bidiyon Ganduje
Asali: Twitter

Mun samu labari shekaran jiya cewa wani Lauya a Najeriya ya na neman hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa watau EFCC ta ba sa ainhin faye-fayen bidiyon da ake zargin an ga gwamnan Kano yana karbar rashawa.

Wannan babban Lauya, Audu Bulama-Bukarti, ya aikawa hukumar EFCC takarda inda ya nemi ya ga bidiyoyin da jaridar Daily Nigerian ta saki kwanakin ana zargin Abdullahi Ganduje da karbar daloli na rashawa daga hannun ‘yan kwangila.

KU KARANTA: Ana karar wani Gwamna da amfani da takardun bogi wajen shiga takara

Barista Audu Bulama-Bukarti, wanda ya shahara wajen karbowa mutane hakkin su a Kano, ya dogara ne da sashen na I na dokar FOI watau Freedom of Information, wanda ya ba ‘dan kasa neman wani bayani daga hannun gwamnati ko wani.

Bulama-Bukarti yana bukatar hukumar EFCC ta aika masa da binciken da ta gudanar game da ingancin wadannan bidiyoyi da aka saki kwanakin baya. A baya EFCC tayi alkawarin cewa tana binciken sahihancin wadannan faye-fayen da aka fitar.

Lauyan ya fadawa hukumar ta EFCC cewa idan har aka yi mako guda ba tare da an aiko masa da abin da binciken da aka gudanar ya nuna ba, zai dauki matakin da ya dace kamar yadda wani sashe na dokar da ta kafa FOI ya nuna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel