Zabe: INEC ta warware kokonto ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa

Zabe: INEC ta warware kokonto ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana kwarin guwar da ta ke da shi a kan sabbin na’urorin tantance ma su zabe da za a yi amfani da su a zabukan shekarar 2019 da za a fara a karshen makon nan da mu ke ciki.

A wata da aka yi da Mista Festus Okoye, kwamishina a INEc sannan shugaban kwamitin wayar da kan ma su zabe, ranar Asabar a Abuja y ace yana da yakinin cewar na’urorin na da inganci kwarai da gaske.

Okoye ya bayyana cewar an inganta na’urorin tantancewar domin samun damar yin aiki cikin natsuwa da karancin matsaloli.

Kazalika, ya kara da cewa INEC ba ta tsammanin cewar sabbin na’urorin za su bayar da wata tangarda yayin aiki da su lokcin zabe.

Zabe: INEC ta warware kokonto ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa
Na’urar tantance ma su zabe
Asali: Facebook

An inganta batirin sabbin na’urorin domin a dade ana aiki da su a wuraren da babu wutar lantarki. An inganta manhajar da ke karanta zanen dan yatsan jama’a.

“wadannan sabbin na’urori da za a yi amfani da su lokacin zabe, su na da inganci fiye da na baya, saboda haka ba ma tsammanin za su bayar da matsala yayin aiki da su. Ko da za a matsala da su, za ta kasance maras yawa.

DUBA WANNAN: Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

“Wannan karon za a samu raguwar matsalar karanta zanen dan yatsan ma su zabe da na’urorin ke bayar wa lokacin zabe,” a cewar Okoye.

Okoye ya kara da cewar INEC ta tabbatar da ingancin na’urori tare da bayyana cewar hukumar ta tanadi yawan na’urorin da za su wadata domin gudanar da zabe a fadin kasar nan.

Mu na da isassun na’urorin tantance ma su zabe kuma mu na Karin wasu na ko-ta-kwana. Tuni an raba wadannan na’urori zuwa jihohi. Bamu da wani kokonto a kan na’urorin mu,” A kalaman Okoye, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel