An kashe dan jaridar nan da ya tona masu cin hanci har lahira a Ghana

An kashe dan jaridar nan da ya tona masu cin hanci har lahira a Ghana

- A jiya da dare ne wasu mutane suka halaka dan jarida Hussein-Suale na kasar Ghana

- Ana zargin wani mahukuncin kasar da kisan sakamakon barazana ga rayuwar dan jaridar da yayi

- Anyi kira ga hukumomin Ghana dasu gaggauta binciko masu hannu a kisar tare da gurfanar da su don adalci ga iyalin shi

An kashe dan jaridar nan da ya tona masu cin hanci har lahira a Ghana
An kashe dan jaridar nan da ya tona masu cin hanci har lahira a Ghana
Asali: Instagram

Wadanda suka dau wani dan jaridan binciken laifuka a boye a kasar Ghana suna zargin anyi mishi kisan gilla inda aka harbe shi a daren laraba.

Ahmed Hussein-Suale na kan hanyar shi ta komawa gida ne inda wasu yan bindiga akan babur suka budewa abun hawan shi wuta a yankin Madina na birnin Accra, sun harbe shi a waurare uku inda suka barshi a mace.

Mista Hussein-Suale babba ne a cikin wata kungiyar yab jaridu masu binciken laifuka tare da Anas Aremeyaw' idon damusa' a kasar Ghana.

Da jimami Mista Anas ya sanar da mutuwar a safiyar alhamis, cewa an harbi marigayin abokin aikin nashi ne so biyu a kirji sai daya a wuya.

A wani faifan bidiyo da Mista Anas ya dora a tuwita a ranar alhamis ya nuna wani mahukunci na kasar Ghana na barazana ga rayuwar Mista Hussein-Suale.

Kennedy Agyapong yace a faifan bidiyon, yace ya ba jama'a damar yin maganin Mista Hussein-Suale wanda hakan zai jawo kyauta mai girma.

GA WANNAN: Azabar da suka gana min ce ta kaini yarda nayi laifin da ban yi ba

Barazanar Mista Agyapong da kuma cewa makasan Hussein- Suale basu dauki komai daga gurin shi ba yasa "Idon damisa" yanke hukuncin cewa aiko su akayi su kashe shi.

Barazanar Mista Agyapong da kuma cewa makasan Hussein- Suale basu dauki komai daga gurin shi ba yasa "Idon damisa" yanke hukuncin cewa aiko su akayi su kashe shi.Barazanar Mista Agyapong da kuma cewa makasan Hussein- Suale basu dauki komai daga gurin shi ba yasa "Idon damisa" yanke hukuncin cewa aiko su akayi su kashe shi.

Mista Anas da kungiyar shi sun shiga sun fita bangarori da dama na ma'aikatun Ghana don binciko rashawa, har da bincike a 2015 da ya fallasa wasu masu Shari'a na karbar cin hanci na kudi, wanda hakan ya jawo sai da suka aje aiyukan su.

Wani binciken sirri a masana'antar wasanni ta Ghana da Hussein-Suale yayi ita ake zargi tayi sanadin rayuwar shi a daren jiya.

A shekarar da ta gabata ne, 'idon damisa' ya bayyana yanda ma'aikatan shi suke samun barazana akai akai, inda yayi kira ga duniya da ta ja musu gaba don tabbatar da hukumomin tsaro na Ghana sun tsaya don tsare rayukan su.

Masu kare hakkin mutane na kafafen yada labarai sunce hakan ya tunatar da duniya irin tsaka mai wuya da hatsari da yan jaridar Afirka ke ciki.

Kwamitin aiyukan yan jarida ta yi ala wadai da kisan Mista Hussein-Suale kuma tayi kira ga hukumomin Ghana da su hanzarta bayyanawa tare da gurfanar da duk mai hannu a kisan gaban kuliya don adalci ga iyalan shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel