Ba zan zabi Inyamurin daya kashe Sardauna da Tafawa Balewa a 2019 ba – Sheikh Yahaya Jingir

Ba zan zabi Inyamurin daya kashe Sardauna da Tafawa Balewa a 2019 ba – Sheikh Yahaya Jingir

Wani yanayi mai daukan hankali musamman a wannan lokaci da zabukan shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, an jiyo shugaban kungiyar Izalatin bidi’a wa iqamatissunnah na bangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wanda zai zaba a matakin shugaban kasa.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani, Datti Assalafiy ne ya bayyana rahoton zancen malamin a shafinsa na Facebook, inda yace sheikh Jingir ya bayyana cewar babu yadda za ayi ya zabi inyamuri, wanda sune suka kashe tsohon firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.

KU KARANTA: Ana dara ga dare yayi: Ma’aikata sun fara yajin aiki a wannan jahar kwanaki 30 kafin zabe

Ba zan zabi Inyamurin daya kashe Sardauna da Tafawa Balewa a 2019 ba – Sheikh Yahaya Jingir
Atiku da Obi
Asali: Twitter

Haka nan ya cigaba da fadin bai ga dalilin da zai sa shi da hankalinsa da lafiyarsa ya zabi duk wani dan siyasa daga kabilar Ibo ba, kabilar da ta kashe tsohon firai ministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa ba.

Sai dai Shehin Malamin ya yi nuni da cewa a fahimtarsa, zai iya zaban shugaban daya jajirce wajen kwato kudaden al’ummar Najeriya da wasu barayi suka yi awon gaba dasu a baya, suna kaiwa kasashen Turawa.

“Ni a ra’ayina, b azan yarda na zabi Inayamurin da ya kashe Sardauna ba, ya kashe Abubakar Tafawa Balewa ba, kuma suka kawo mana yakin basasa a kasarmu mai albarka ba, amma zan zabi wanda ya dawo mana da kudin da wasu barayin kasarmu suka sace suka kaiwa turawan yamma.” kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito shi.

Idan za’a tuna, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben dake zuwa, sai dai mataimakinsa Peter Obi inaymuri ne daga jahar Anambra, amma a bayyana take shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwato kudaden da barayi suka sace, don haka duk wanda ya yi magana a kasuwa ya san da wanda yake.

Wannan ra’ayi na Sheikh Jingir ya ci karo da na mataimakinsa, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, wanda a kwanakin baya ya bayyana cewa shi kam Atiku Abubakar zai zaba saboda yana da kishin musulunci, ya gina Masallatan juma’a sama da hamsin.

Amma da yake siyasa rigar yanci ce, dole ne a girmama ra’ayin kowa daga cikinsu, musamman ta yadda duk da takaddamar dake tsakanin Izalar Jos da ta Kaduna a karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau, amma sun dauki matsayi guda game da zaben Buhari a 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel