Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce

Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce

- Kungiyar matasan kiristoci karkashin reshen jihar Bauchi ta kushe jita jitar da ake yadawa

- Kungiyar tace bata furta cewa tana goyon bayan sake zaben gwamnan jihar ba

- Kungiyar ba kungiyar siyasa bace

Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce

Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce
Source: UGC

Kungiyar matasan kiristoci ta kasa reshen jihar Bauchi ta wanke kanta daga rahoton cewa kungiyar kiristoci ta kasa akan cewa suna goyon bayan sake zaben gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar.

A wata takardar da kakakin kungiyar yasa hannu, Comrade Daure David Yankoli ya bawa manema labarai a ranar lahadi, 30 ga watan Disamba,2018 cewa kungiyar ta wanke kanta daga goyon bayan gwamnan wanda Rev Joshua Ray Maina, shugaban kungiyar a ziyarar kirsimati da suka kai gidan gwamnatin jihar.

Takardar ta kunshi, "An jawo hankalin kungiyar matasan kiristoci da kafar watsa labarai ta CAN ta sanar da cewa kungiyar tana goyon bayan kara zaben gwamnan jihar a zaben 2019 mai zuwa."

Kakakin kungiyar ya kushe tare da wanke kansu daga wannan batu domin kungiyar su ba ta siyasa bace.

DUBA WANNAN: Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

Ya nuna rashin jindadin shi akan maganar goyon bayan kuma yayi alkawarin tabbatyda adalci a mulkin, yana cewa "Muna sukar wannan labarin domin zai iya rage mana kima. Bazamu tankwashe kafa muna kallo wasu mutane kadan su bata mana suna tare da zubar mana da mutunci ba. Addinin kirista yafi kowanne mutum girma."

Takardar ta karanta kamar haka, "Dukkanin mu masu shugabanci munji labaran da ake ta yadawa tare da wallafawa akan mu Wanda ba gaskiya bane. Saka kiristoci a irin wannan batu na siyasa hatsari ne kuma dole a daina saboda ana saka dangantakar mu da cigaban jihar da kasar baki daya a hatsari."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel