Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo

Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo

- Zobo ko Karkady ya zama abin sha ko a matsayin shayi ku a matsayin lemo

- Soborodo dai a kasashen mu ake shansa

- Babu wata ma'aikata da ta sahale ake sayar dashi

Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo
Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo
Asali: Facebook

Professor na Physiology, Ibiyemi Olatunji-Bello, tsohon vice-chancellor, na Lagos State University College of Medicine, wadda ke Legas, yayi kira ga jama'a da su farga da sabbin abinci da 'yan Najeriya ke dumfafa ko don sana'a ko don nishadi, inda yace dole sai an binciki sinadaran da suke kunshe dashi.

A Najeriya dai, Soborodo lamurje ne da kowa ke sha, wanda akan sha shi kamar shayi da safe ko dare, wasu kuma sun fi sonsa a mtasayin lemo inda akan hada shi da lemon tsami, siga, ko kayan alatu irinsu abarba ko ma flavor don kamshi.

DUBA WANNAN: Ko N500 daya babu a jikin Alex Badeh sanda ya rasu, iyalansa sun karyata 'yansanda

A cewar likitan, sai an kula, domin kuwa idan mata suka sha shi, yana da illoli da yake sanya musu a jikinsu, ko ta kara kiba, ko ya hana balagar mace da wuri.

Yace wannan illar ta ma fi yawa a kan masu ciki mata da masu shayarwa, inda hakan kan kwari yaran nasu ko tun suna ciki ko suna tasowa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel