Na kama kwarto turmi da tabarya da matata - Magidanci ya sanar da kotu

Na kama kwarto turmi da tabarya da matata - Magidanci ya sanar da kotu

- Watan kotun al'adu dake Ibadan, ta warware auren shekaru takwas, tsakanin Adedolapo Aderibigbe, wani jami'in safiyo, da matarsa, Mayowa

- Alkalin kotun, Ademola Odunade, ya ce ya warware auren ne sakamakon zargin cin amana da barazana ga rayuwa da suka mamaye auren

- Kotun ta mika kulawar yara uku da aka samu a auren ga Mayowa, yayin a shi Adedolapo zai rinka biyanta N12,000 a kowanne wata don kula da yaran

Alkali Ademola Odunade, shugaban kotun al'adu ta Mapo da ke Ibadan, a ranar Alhamis, ya warware wani aure na shekaru 8 tsakanin Adedolapo Aderibigbe, wani jami'in safiyo, da matarsa, Mayowa, sakamakon zargin cin amana da barazana ga rayuwa da suka mamaye auren.

Odunade, wanda ya ce batutuwa kan zargin cin amana da barazana ga rayuwa a cikin auratayya, na zamowa abun sanya damuwa a cikin zuciya, ya ce akwai bukatar ma'aurata su kasance masu jin tsoron Allah a cikin zamantakewarsu.

"Domin wanzar da zaman lafiya a rayuwa, zaman auratayya tsakanin Adedolapo da Mayowa, a yau yazo karshe. Don haka tarbiya da kulawar yara uku da aka samu a auren zai koma hannun Mayowa, yayin a shi Adedolapo zai rinka biyanta N12,000 a kowanne wata don kula da ci da tufatarwar yaran da kuma daukar nauyin karatunsu," a cewar alkalin.

KARANTA WANNAN: Kiwon lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa - Rahoton UAE

Na kama kwarto dare dare a kan matata - Magidanci ya sanar da kotu
Na kama kwarto dare dare a kan matata - Magidanci ya sanar da kotu
Asali: Depositphotos

Da yake mayar da martani kan zargin da matarsa tayi masa na yin barzana ga rayuwarta, Adedolapo ya shaidawa kotun cewa matar ta fadi hakane kawai don borin kunya akan zainace zainacen da take yi da wasu mazan a waje.

Haka zalika ya bayyana cewa dama dai tuni Mayowa ta shaida masa cewa wata rana zata mayar da 'yayan uku ga ubansu na asali, wanda kuma shi da kansa ya sha kamata da kwataye, wanda kuma a gaban jama'a ta durkusa akan guiwowinta ta roke shi gafara.

Sai ita a nata bangaren, Mayowa ta jaddadawa kotun cewa mijin nata yasha yi mata barazana da wasu muggan makamai, bayan dan karen dukan da take sha a hannunsa. Wanda har iyayenta da makwaftansu suka gaji da shiga tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa ma'auratan na zaune ne a yankin Apete dake jihar Ibadan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel