Hatsari: Gobarar tankar dakon man fetur ta hallaka mutane 3 a Fatakwal

Hatsari: Gobarar tankar dakon man fetur ta hallaka mutane 3 a Fatakwal

Mutane uku sun mutu da sanyin safiyar yau, Talata, a unguwar GRA phase 4 dake garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas bayan tashin wata gobara sakamakon tsiyayar man fetur daga wata motar dakon man fetur.

Shaidun gani da ido sun shaidawa legit.ng cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na safiyar yau bayan motar dakon man fetur din ta fadi kuma man dake cikinta ya kwarara zuwa gine-ginen dake daf da inda ta fadi.

A kalla jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya 190 ne suka kauracewa aiki bayan an tura su zuwa jihar Borno domin yaki da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Damuwa da wannan hali da jami'an da suka nuna ne ya saka hukumar 'yan sanda bayar da umarnin kamo su tare da gurfanar da su.

A wani rahoto da Saharareporters ta wallafa, jaridar ta ce majiyarta ta sanar da ita cewar jami'an sun kauracewa aiki ne saboda tura su yaki ba tare da basu horo ba. Kazalika, majiyar ta ce sun yi korafin cewar da yawansu mabiya addinin Kirista ne da suka fito daga yankin kudu.

Hatsari: Gobarar tankar dakon man fetur ta hallaka mutane 3 a Fatakwal

Hatsari: Gobarar tankar dakon man fetur ta hallaka mutane 3 a Fatakwal
Source: Facebook

"Sun kauracewa aiki ne saboda tura su jihar Borno cikin gaggawa domin yaki da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram ba tare da basu wani horo ba," cewar majiyar.

Sannan ta kara da cewar, "ku san dukkansu 'yan kudancin Najeriya ne kuma kaso 96% daga cikinsu mabiya addinin Kirista ne. Wannnan batu ya matukar tayar da kura a hukumar 'yan sandan Najeriya."

Sai dai, hukumar 'yan sanda ta bayar da rahoto sabanin wannnan, inda ta ce jami'an MOPOL 22 ne suka kauracewa wurin aikin basu horo ne a gain Buni-Yadi, kamar yadda yake cikin wata sanarwar da Saharareporters ta gani.

DUBA WANNAN: Sarkin Tsafe ya bayar da umarnin cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

Ana tunanin jami'an MOPOL din 190 na daga cikin rundunar 'yan sanda 2,000 da babban Sifeton 'yan, Ibrahim Idris, ya tura zuwa yankin arewa maso gabas domin yin aikin soji na dakile tare murkushe aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Da yake tabbatar da tura rundunar jami'an tsaron, Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya ce akwai jami'an 'yan sanda daban-daban a cikinta da suka hada da PMF, CTU, da kuma kwararru wajen amfani da karnukan hukumar 'yan sanda na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel