Tsafi karara: Hankula sun tashi yayin da wata matar aure ta rika aman sabbin kudi a Najeriya

Tsafi karara: Hankula sun tashi yayin da wata matar aure ta rika aman sabbin kudi a Najeriya

Wata matan aure Mariam Abdul, a ranar Lahadi ta yi aman sabbin naira N500 bayan wasu wadansu da ake zargi matsafa ne sun sace ma ta ‘yan kanfanta 2 a kuayen Effurun da ke karkashin karamin hukumar Uvwie a jihar Delta.

An samu labarin cewa abun ya faru ne a ta yankin JJC da ke Effurun, wanda faruwar hakan ya saka mazauna yankin cikin wani hali.

Tsafi karara: Hankula sun tashi yayin da wata matar aure ta rika aman sabbin kudi a Najeriya

Tsafi karara: Hankula sun tashi yayin da wata matar aure ta rika aman sabbin kudi a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ba wanda zai kara shiga rigar Buhari a 2019 - PDP

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa ita wannan matar wacce ta ke tsakanin shekaru 20 da wannan abu, ta shanya kanfanta a waje ne bayan ta gama wanke su a makonni 2 da suka gabata amma kawai sai ta fara aman sabbin N500 a ranar Lahadi da safe a yayin da mijinta, Taye Adekunle, ya neme agajin al’umma.

Wani mutum wanda ya shaida faruwar abun ya ce kafin faruwar hakan, Mariam tana zargin wasu matsafa ne wadanda ke zagayawa a yankuna daban daban a fadin jihar suna satan kanfan mata suka sace ma ta ‘yan kanfanta.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar mai rikon kwarya, DSP Andrew Aniamaka, ya tabbatarwa manema labarai da faruwar hakan.

DSP Aniamaka ya ce, “Mun samu labarin hakan daga ofishin ‘yan sanda na “B” Division. Jami’an mu sun fara gudanar da bincike a kan lamarin. Idan akwai wani alamar gaskiya a lamarin za mu sanar ma ku da anjima.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel