Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019

Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019

- Wata kotun majistare ta bada damar tsare Mista Adeyanju har zuwa watan Fabrairu

- Hakan ya sabawa dokar kundin tsarin mulki inji Lauyan shi

- A halin yanzu wasu abokan shi sun shigar da kara a wata kotun tarayya, inda kotun ta bada umarnin sakin shi

Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019
Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019
Asali: Depositphotos

Wata kotun majistare ta bada umarnin tsare Deji Adeyanju a gidan kaso har zuwa watan Fabrairu na 2019, bayan Jin rokon shi da kuma rashin karfin yanke hukunci akan kisan da ake zargin shi da shi.

Yan sanda sun kama Mista Adeyanju ne a ranar 13 ga watan Disamba, sakamakon zargin shi da ake da kisan kai.

Amma majiyar mu ta tabbatar mana da cewa wata babbar kotun jihar Kano ta sake shi tare da wanke shi bayan doguwar shari'a tsakanin 2005 zuwa 2009.

Yan sanda a Abuja sun tsare Mista Adeyanju na kwanaki biyar wanda daga baya suka maida shi kano a farkon satin nan.

Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019
Kotu a Kano ta rufe dan siyasa a sijin har sai bayan zabe a Feb. 2019
Asali: Depositphotos

'Yan sanda a jihar Kano sun gurfanar da Adeyanju gaban Hassan Fagge a ranar 19 ga watan Disamba, amma sai aka umarci da a tsare shi. Amma da kotu ta Bude da karfe 9:42am na ranar juma'a, Mista Fagge yace ya yanke cewa bashi da karfin sauraron abubuwan da ake zargin Mista Adeyanju dashi, amma a cigaba da tsare shi har zuwa 6 ga watan Fabrairu da babbar kotun zata iya sauraron shari'ar.

An maida Mista Adeyanju babbar gidan kaso ta Kano, Lauyan shi, Yusuf Suleiman, ya sanar da majiyar mu da ranar juma'a, rashin dacewar takura babban kalubale a sati kadan da ya rage na zabe.

"Wannan kiri kiri yunkurin ajiye shi ne ba bisa ka'ida ba," Mista Suleiman yace, ya kara da cewa an gama shari'ar tun kusan shekaru 10 da suka wuce, bai kamata yan sanda, balle kuma komar dashi kotu.

Mista Suleiman yace yan sandan Kano na wasan siyasa da hakkin Mista Adeyanju wanda babban zagi ne ga kundin tsarin Najeriya.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

Bayan ajiye shi a Abuja na kwanaki ba tare da an kaishi gaban shari'a ba wanda kundin tsarin mulki sa'a 48 ya bada dama, yanzu kuma zargin shi ake da yunkurin kisan kai wanda mai shari'ar yace bashi da karfin ji," inji Mista Suleiman.

Lauyan yace za'ayi kokarin ganin an saki Mista Adeyanju kafin 6 ga watan Fabrairu da za'a ji karar, hadi da tunkarar babbar kotu don kara duba shari'ar.

Wasu abokan Mista Adeyanju sun mika kara ga wata kotun tarayya a Abuja saboda danne mishi hakki da aka yi.

Adebayo Raphael, Daya daga cikin masu yakin neman sakin Mista Adeyanju, yace babbar kotun tarayya a Jabi ta umarci da a gaggauta sakin Mista Adeyanju.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel