Abubuwa goma da za'a hanga kafin zaben 2019, daga Dr. Abdurrazak Ibrahim

Abubuwa goma da za'a hanga kafin zaben 2019, daga Dr. Abdurrazak Ibrahim

- Kimiyya da fasaha a halin yanzu sune ke kawo cigaba

- Saka mata tsundum a harkokin kasar nan zai iya kawo cigaba

- Muna fatan ganin gwamnatin da zata yaki tsananin talaucin dake damun kasar nan

Abubuwa goma da za'a hanga kafin zaben 2019, daga Dr. Abdurrazak Ibrahim
Abubuwa goma da za'a hanga kafin zaben 2019, daga Dr. Abdurrazak Ibrahim
Asali: Original

Akwai abubuwan masu muhimmanci da ya kamata masu burin shugabantar mu a 2019 su duba.

1. Canjin yanayi da abubuwan da zai iya haifarwa a siyasa da tattalin arziki: Wasu manyan kasashen na daukar canjin yanayi a matsayin karamar magana wanda hakan yaci karo da fahimtar masana kimiyya. Muna bukatar shuwagabannin da zasu duba kimiyya gurin kawo cigaba tare da tabbatar da cigaban.

2. Kare hakkin dan-adam tare da hana cin mutuncin mutane: Da farko dai, kare hakkin dan-adam ba yana nufin kare 'yan ta'adda bane. Yana nufin mutunta rayuka tare da kirkinta su duk kuwa da sabanin ra'ayi ko fahimta da ya shiga tsakanin ku. Kowanne jami'in gwamnati ko dan kasa ya gane hakan.

3. Gujewa hanyoyin halaka da sunan addini: Cigaban kimiyya tare da tunani musamman ga matasa zai iya kawo juriya da kuma fahimtar cewa kowanne addini ra'ayoyi ne. Wannan zai sa a gane hada addinai da siyasa na da hatsari kuma kan hana cigaba.

4. Ilimi da kirkire-kirkire : Muna fatan ganin gwamnati a 2019 mai cike da jajirtattu da kwararru. Wannan ce irin gwamnatin da zata sadaukar da komai gurin canza makarantun mu da suke yaye "zauna-gari" zuwa ga makarantun da zasu zamo cibiyoyin koya da bincike ta hanyar amfani da abubuwan da muke dasu a nan gida.

DUBA WANNAN: Yawan marasa aikin yi qaruwa yayi daga bara zuwa yanzu a sabuwar kididdigar NBS

5. Kawo karshen tsananin talauci: Karin kokari gurin ilimantar da matasa da mata tare ta karfafar su da tallafa musu. Dole ne a karfafa kasar mu ta hanyar koya ma matasa da mata sana'o'i da abubuwan da suke da shi. Akwai kirkire Kirkire da zasu iya gyara rayukan mutane tare da kawo karshen tsananin talauci.

6. Saka mata tsundum a kowacce harka ta cigaban kasa: Mace ba wai rayuwar ta a madafi zata kare ba. Yakamata a bata dama tayi rayuwar ta a inda take so. A makaranta, ofishi, kasuwa ko ma zama shugaban kasa ne. Sannan kuma duk abinda mutum mai hankali zai yi da jikin shi bai zama damuwar gwamnati ba ko wata cibiyar.

7. Dole a gina kasa, ba a gina mutane ba. Maimakon ace akwai manya a siyasa da mulki, yafi dacewa ace a gina ma'aikatu, bangarori, kamar na sharia, lafiya, tsaro, ilimi, da ma dokoki.

8. Fahimtar da jama'a inda duniya ta nufa, maimakon yadda muke a yankunanmu babu alkibla, bamu ma fahimci ina matsalar take ba balle mu san warware ta.

9. Koyawa 'yan siyasarmu yadda sauran kasashe suka iya haurar da jama'arsu daga qangin bauta da ci baya, da talauci, kamar yadda Rasha da su China suka yi, kamar yadda turawa da wasu kasashen Afirka suka yi.

10. Qara wanda kuma kuke ganin shine zai zamo na goma a lissafin...

Abdulrazak Ibrahim, PhD (biorazi@gmail.com)

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel