Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga dadi sun halbe Alex Badeh har lahira

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga dadi sun halbe Alex Badeh har lahira

Wasu 'yan bindiga dadi da ba'a san ko suwaye ba sun harbe tsohon hafsan hafsoshin dakarun sojojin Najeriya Air Vice Marshal Alex Badeh har lahira akan hanyar sa ta dawowar daga gonar sa akan Abuja zuwa Keffi da daren yau.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibukunle Daramola ya fitar ranar Talata da daddare ta ce 'yan bindigar sun kai hari kan motar da Mr Badeh ke ciki lokacin da yake dawowa daga gonarsa a kan titin Abuja-Keffi.

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga dadi sun halbe Alex Badeh har lahira

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga dadi sun halbe Alex Badeh har lahira
Source: Facebook

KU KARANTA: Na shirya gamuwa da mahalicci na - Buhari

A cewar sojin, tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji daga harbin bindigar da aka yi masa.

Alex Badeh ya rike mukamai da dama na soji, ciki har da babban hafsan sojin sama da babban hafsan tsaron Najeriya.

A lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram, mayakan kungiyar sun kai hari a kauyensu, ViMtim da ke jihar Adamawa.

Cikakken rahoto kan labarin na nan tafe..

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel