Hukumomin tsaro da na gargajiya sunyi taron duba yadda za'a kassara tashin-tashina bayan zabe

Hukumomin tsaro da na gargajiya sunyi taron duba yadda za'a kassara tashin-tashina bayan zabe

- Yunkurin iyar da zabukan 2019 cikin lumana da nasara

- Anyi taron 'yansandan Najeriya da masu ruwa da tsaki a zaben 2019

- Taron ta samu halartar Shugaban EFCC, Ibrahim Magu

Hukumomin tsaro da na gargajiya sunyi taron duba yadda za'a kassara tashin-tashina bayan zabe
Hukumomin tsaro da na gargajiya sunyi taron duba yadda za'a kassara tashin-tashina bayan zabe
Asali: UGC

Domin samun yin zabe cikin lumana tare da zama lafiya bayan an saki sakamako, dole ne a fara shirye shirye da wuri. Don bahaushe yace, tun jiya ake pape gorar tafiyar jibi.

Wannan yana daya daga cikin shirye shiryen da akeyi tsakanin 'yan sandan Najeriya da masu ruwa da tsaki akan tsaro, kafin, lokacin da bayan zaben.

Taron mai taken "Tsaro yayin zabe: Hadin guiwa tsakanin 'yan sandan Najeriya da masu ruwa da tsaki don yin zabe mai nasara a 2019" ya samu halartar Mukaddashin Shugaban EFCC, Ibrahim Magu. da ma shugabannin gargajiya na al'ummu da dama,

Anyi taron ne a International Conference Centre dake Abuja.

DUBA WANNAN: Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana

Saboda matsalar Najeriya, gabas da yamma, kudu da arewa, kabila da yaruka, addinai da dariqu, da ma 'yan zaman kansu, dole ne a sami turba guda ta bin kadin zaben domin watakil ba lallai sakamakon ya farantawa wasu rai ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel