Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo

Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace wadanda ke ta fatar mutuwar shi, sune ke adawa dashi

- Ba raye cikin koshin lafiya kawai yake ba, har da zabe mai zuwa zai lashe inji Osinbajo

- Kamar yanda kuke gani, akwai hadin kai a adawar

Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo
Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace wadanda ke ta fatar mutuwar shi sune yanzu suke adawa dashi. Mista Yemi Osinbajo yace ba wai a raye da lafiya kadai shugaban kasar yake ba, har zaben 2019 zai lashe.

Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo
Mun gano wani sabon taron dangi na karkashin kasa kan Buhari - Osinbajo
Asali: Twitter

"Dukkansu sun hade kansu saboda mutum daya, shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma suna da hadin guiwar su a ko ina. A kasuwanci, siyasa, addini da ma ko ina. Sun ta addu'ar ya mutu, sai suka ga ya dawo da rai da lafiya fiye da da."

Mista Osinbajo yace mutanen sun kalubalanci cibiyar habakawa ta Gwamnatin tarayya mai suna TradeMoni.

DUBA WANNAN: Kisan jami'an tsaro a Arewa maso yamma, abin tsoro ne ko kuma tsohon lamari ne?

"Kowanne lokaci akayi magana sai ranar ya baci amma Idan aka ce Tallafawa masu karamin karfi sai dai shaidanu ne zasuyi wani koken akan TradeMoni".

Da yawa dai daga manyan kasar nan, sun ki su lamuncewa shugaba Buhari yayi tazarce, inda su kuma talakawa sunka ce sunji sun gani sai ya zarce.

Akwai alamun dai, koda shugaba Buhari zai lashe zaben na 2019, to fa lallai zai sami kalubale daga Atiku, wanda tsohon dan siyasa ne kuma mai alamun kawo sauki.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel