Manyan Darikar Katolika sun yi fushi da Fasto Mbaka saboda sukar Atiku

Manyan Darikar Katolika sun yi fushi da Fasto Mbaka saboda sukar Atiku

- Manyan 'Yan Darikar Katolika sun fusata da sukar Atiku da Obi da Mbaka yayi

- Darektan Katolikar Kirista yace babu wanda ya aiki Faston yayi wannan aiki

- Akwai dai yiwuwar Shugabannin Kiristan su hukunta fitaccen Malamin adiinin

Manyan Darikar Katolika sun yi fushi da Fasto Mbaka saboda sukar Atiku

Jagororin Darikar Katolika sun nesanta kan su daga danyen aikin Mbaka
Source: UGC

Mun samu labari daga Jaridun Kasar nan cewa babban Limamin cocin na Katolikan Najeriya da ke Jihar Enugu, Rabaren Ejike Mbaka ya jawowa kan sa fushin Shugabannin ‘Darikar Katolikan Kasar nan da wasu kalaman sa.

Kwanan nan ne babban Limamin ya caccaki ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma Abokin takarar sa watau Peter Obi. Rabaren Fr. Mbaka yace babu abin a-zo-a-gani da Peter Obi yayi wa addinin Kirista.

KU KARANTA: Wani Malamin addinin bogi ya shiga hannun Jami’an tsaro a Legas

Darektan sadarwa na Darikar Katolikan Enugu watau Rabaren Benjamin Achi ya bayyana cewa Cocin ba ta goyon wannan danyen aiki da Rabaren Mbaka yayi. Benjamin Achi yace sam ba aikin Limamai bane shiga hurumin siyasa.

Benjamin Achi, wanda yayi magana a madadin Jagororin Darikar ta Kirista ya bayyana cewa dokar su ta haramtawa Limami ya rika yin jawabi game da abin da ya shafi siyasa don haka akwai yiwuwar a hukunta Mbaka na sabawa doka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel