Hadin Kai tsakanin Musulmi da Kirista shine zaman lafiyar Najeriya - Buhari

Hadin Kai tsakanin Musulmi da Kirista shine zaman lafiyar Najeriya - Buhari

- Shugaba Buhari ya yi korafi kan zarginsa da yunkurin Musuluntar da Najeriya

- Shugaban kasa Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya su hankalta da masu yunkurin raba kasar nan

- Shugaba Buhari ya yi fadakarwa kan siyasantar da addini

- Hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista zai tabbatar da ci gaban Najeriya

Za ku ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi ga al'ummar kasar nan baki daya dangane da siyasantar da addinin inda a cewar sa hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista zai tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wani rubutaccen sako na bayyana ra'ayi a bisa mahanga ta addini da kamfanin jaridar Church Times ya wallafa kasancewarta babbar jarida kasar Birtaniya dake kan darikar Anglican a addinin Kirista.

Sakon da jaridar ta gabatarwa manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata cikin babban birnin kasar nan tarayya ya zayyana cewa, shugaba Buhari ya yi kira kan hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista da tasirin hakan zai fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira.

Hadin Kai tsakanin Musulmi da Kirista shine zaman lafiyar Najeriya - Buhari

Hadin Kai tsakanin Musulmi da Kirista shine zaman lafiyar Najeriya - Buhari
Source: Depositphotos

Rahotanni a baya can dangane da adawa sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari na yunkurin amfani da kujerarsa ta iko wajen Musuluntar da kasar nan da ko shakka ba bu hantsi ya dubi ludayi a halin yanzu dangane da wannan tuhuma ga shugaban kasa.

Kamar yadda shafin jaridar Guardian ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya kuma gargadi al'ummar kasar nan dangane da kauracewa rabuwar kai da nuna bambancin akidar imani cikin harkokin siyasar kasar nan da a cewar sa sai an hada kai tare domin cimma nasara.

KARANTA KUMA: Rashin sa'ar samun masu gida, wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon suna nan dawowa

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya kuma bayyana takaicinsa gami da damuwa dangane da yadda 'yan adawa ta siyasa ke yunkurin amfani da bambance-bambance na addini wajen raba kawunan al'umma.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar ta Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a Yammacin yau ta Asabar shugaban kasa Buhari ya shilla kasar Poland domin halartar taron Majalisar dinkin duniya karo na 24 kan sauyin yanayi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel