Duniya tayi wa kasar China caa, kan tace addinin Islama tabin hakali ne, ta kuma kame miliyoyin musulmi ta rufe

Duniya tayi wa kasar China caa, kan tace addinin Islama tabin hakali ne, ta kuma kame miliyoyin musulmi ta rufe

- Daular Islama zamanin Khalifofi ta kai har kasar Sin

- Har yanzu jihohin yammacin China musulmi ne na kabilar Uiyghur/Wigar

- Kasar China ta kafa manyan sansanoni a sassa daban daban na kasar

Duniya tayi wa kasar China caa, kan tace addinin Islama tabin hakali ne, ta kuma kame miliyoyin musulmi ta rufe
Duniya tayi wa kasar China caa, kan tace addinin Islama tabin hakali ne, ta kuma kame miliyoyin musulmi ta rufe
Asali: Instagram

Kungiyoyin kare hakkokin bil-adama, da ma na sauran kasashe da suka san bil-adama, sun hadu suna ta Allah-wadai da katafaren shirin kasar Sin, ta China, na kulle kusan ilahirin kabilun kasar ta kaf a fadin kasar, wadanda tace makaranta ta sanya su.

A zamunnan Khalifofin Islama, lokacin da suke kai hare-hare yankunan duniya da takubba, su kama kasashe, ko dai su musuluntar, ko kuma su bautar, ko kuma su karbi harajin jizya, mujahidan sun kai har kasar China.

Har zuwa yanzu, akwai musulmi da yawa a kasar, wadda take bin tsarin gurguzu, wanda bai yarda da kowanne addini ba, kuma ya kira kowanne addini da yaudara, ya kuma karyata samuwar alloli.

Su dai 'mazan kabilar ta Uyghur, suna son ballewa daga kasar ta China ne, kuma suna son kafa kasar su wadda zasu kira daular Islama, su kuma yi shari'ar Islama.

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur kan kudi

Sai dai kash! BAyan da aka sami kungiyoyi masu irin wannan akida a sauran sassan duniya, sai aka sami samari da yawa da ma malamansu, sun bi wannan akida, wadda Saudiyya ta yada, da Wahabiyyanci da jihadi.

Hukumomin kasar Sin dai, da 'yansandan boye, sunyi ittifaki, wadannan musulmi, sun kudiri aniyar tashin tashina, da zimmar juyin-juya hali, don kifar da gwamnatin gurguzun ta Sin, da kafa daular ISlama. wadda zata bautar da sauran kabilun yankin, da ma fille kawunan mutane, kamar yadda dai ake yi a kasashen Musulmi, ko yankunan 'yan ta'adda.\

Da aka tambayi hukumomin kasar Sin, sai suka ce, ai duk wanda ba zai iya zama da sauran jama'a ba, sai dai ya kira su da kalaman Dhimmi, ko kaskantattu, ya kuma ce jininsu ya halasta, saboda basu bi addinin ko akidar ba, to lallai yana da tabin hankali.

A cewar kasar ta China, tana baiwa wadannan miliyoyin musulmi magunguna ne, da atisaye, da wayar musu da kai, da ma cire musu wannan muguwar aqida ta son kashe waninka, wadda masu ta'addanci.

A yanzu dai, a sassan kasar, an rufe wuraren wasa da makarantu a yankin, da ma masallatai, inda duk akamayar dasu wuraren ajje masu zafin ra'ayi, wanda BBC da Aljazeera ta tabbatar sun kai akalla miliyan ukku.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel