Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taro a kasar Chadi

Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taro a kasar Chadi

A yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daga N'Dajamena, babban birnin kasar Chadi, bayan ya jagoranci taron shugabannin kasashen Afrika dake da makwabtaka da tekun Chadi (LBC)

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar Buhari ya yi amfani da matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen wajen kiran taron domin tattauna yadda za a samu zama zaman lafiya mai dorewa a rukunin kasashen LBC dake fama da hare-haren 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da Femi Adesina, karamin kakakin shugaba Buhari, ya fitar a Abuja ya ce za a yi taron ne yau, Alhamis, a N'Dajamena.

Boko Haram: Buhari ya tashi zuwa kasar Chadi
Buhari ya tashi zuwa kasar Chadi
Asali: Twitter

Adesina ya bayyana cewar an gayyaci shugaban kasar Benin zuwa wurin taron saboda kasar sa ta bayar da gudunmawar sojoji domin yakar aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

A cewar Adesina, taron na kwana daya zai tattauna yanayin tsaro a tsakanin kasashen da niyyar samar da hanyoyin da za a bi domin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram.

A baya Legit.ng ta rawaito cewar shugaba Muhammadu Buhari ya kalubanci ragowar shugabannin kasashen gefen tekun Chadi (LBC) a kan kara rubanya kokarinsu a bangaren yaki da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram.

Buhari ya yi wannan kira ne a yau, Alhamis, yayin halartar taron shugabannin kasashen gefen tekun Chadi a birnin N'Dajamena.

"Ba zamu saurara ko mu bar makiya yankin mu su sukurkuta zaman lafiya a kasashen mu ba. Dole mu kara kokarinmu domin korar ta'addanci daga yankinmu."

"Dole mu tashi tsaye wajen samar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa. A wannan gaba ne nake bukatar mu hada karfi da karfe domin ganin mun kakkabe ragowar 'yan ta'adda daga yankin mu," a kalaman Buhari.

Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Chadi, Nijar, da Kamaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel