Wutar Gobara ta lashe babbar Kasuwa a jihar Katsina

Wutar Gobara ta lashe babbar Kasuwa a jihar Katsina

Mun samu cewa a jiya Juma'a tsautsayi da ya baya wuce ranarsa ya auku yayin da wutar gobara ta lashe fiye da shaguna 100 a shahararriyar kasuwar nan ta Funtua da ke birnin jihar Katsina kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito.

Har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba bu masaniyar dalilin aukuwar wannan tsautsayi na gobara ta shafe tsawon sa'o'i biyu ta na tafka ta'asa a daren jiya na Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan gobara ta yi babban ta'adi inda ta yi sanadiyar salwanta gami da asarar dumbin dukiya ta miliyoyin Naira.

Wutar Gobara ta lashe babbar Kasuwa a jihar Katsina
Wutar Gobara ta lashe babbar Kasuwa a jihar Katsina
Asali: Facebook

Jami'an hukumar kwana-kwana ta jihar tare da al'umma masu zuciyar jin kai, sun yi azamar gaske wajen bayar da muhimmiyar gudunmuwa ta kashe wutar wannan gobara kamar yadda mashaidanta suka bayyana.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi koyi da Tarihin nasarorin PDP - Jonathan

Mamallaka Shaguna da 'yan Tireda sun dugunzuma wajen killace dukiyarsu da Gobarar ta ci ta rage inda aka yi sa'ar gaske ba bu rai ko guda da ya salwanta.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta samu rahoton cewa, gobarar Daji ta salwantar da rayukan Mutane 84 a Arewacin jihar California da ke kasar Amurka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel