Yanzu-yanzu: Harin Boko Haram a sansanin Soji ya hallaka dakarun soji uku

Yanzu-yanzu: Harin Boko Haram a sansanin Soji ya hallaka dakarun soji uku

Mayakan Boko Haram da ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar ta'addanci na IS (Islamic State West Africa Province) sun kai hari a sansanin Sojin Najeriya a garin Kareto da ke kilomita 150 arewacin Maiduguri.

'Yan ta'addan sun sha karfin sojojin da ke sansanin kafin jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kawo musu dauki daga bisani inda ya tarwatsa 'yan ta'addan.

"Sojoji uku sun riga mu gidan gaskiya kuma akwai wasu da dama da ba mu gansu ba a yanzu," kamar yadda wani jami'in soja da ke Maiduguri ya fadawa AFP.

Da dumi-dumi: Sojin Najeriya 3 sun rasu sakamakon harin da Boko Haram suka kai sansanin soji
Da dumi-dumi: Sojin Najeriya 3 sun rasu sakamakon harin da Boko Haram suka kai sansanin soji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

"Jiragen saman yaki ne suka fattatki 'yan ta'addan," inji sojin da ya nemi kada a bayyana sunansa saboda ba a bashi izinin yin tsokaci kan harin ba.

An turo karin sojoji zuwa sansanin domin su taimaka mana, a halin yanzu bamu san ko sun sace makamai ba inji jami'in sojan.

Wani jami'in civilian JTF ya ce yan Boko Haram din sun gudu zuwa garin Gubio wadda ke kilomita 60 daga Kareto yayinda su kuma mutanen garin Kareto suka rika tserewa Jamhuriyar Nijar.

"An karo sojoji zuwa Kareto amma galibin mutanen garin ba su dawo ba," inji shi.

Wannan dai shine karo na biyo da yan ta'adda ke kai hari a sansanin na Kareto cikin shekaru biyu.

A watan Afrilun 2016, Boko Haram sun kai hari inda suka jikata sojoji 24 kamar yadda hukumar sojin Najeriya ta sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel