Shugaba Buhari yayi magana kan bullar faifan bidiyon hatsabibi Nnamdi Kanu
- Shugaba Buhari yayi magana kan bullar faifan bidiyon hatsabibi Nnamdi Kanu
- Yace wannan ya nuna cewa gwamnati bata kashe shi ba
- Nnamdi Kanu dai ya tsere daga Najeriya ne ta barauniyar hanya
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da martani kan wani faifan bidiyo da yanzu haka yake yawo a a kafofin sadarwar zumunta na zamani dauke da muryar hatsabibin nan Nnamdi Kanu dake zaman jagoran kungiyar IPOB inda a ciki yake cewa zai dawo kasar.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Dalilin da ya sa ba mu kaunar Shugaba Buhari - Gwamna Ortom
Mai taimakawa shugaban kasar ta fannin yada labarai na musamman, Malam Garba Shehu ne ya mayar da martanin inda yace idan har da gaske ne jagoran 'yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra ya yi bayani a bidiyon, to gaskiya ta fara bayyana game da zargin da ake yi mata na salwantar da shi, kuma tana dakon shigarsa kasar.
Legit.ng Hausa ta samu cewa a wani bangaren guda kuma ana ma tababa ne kan ainihin lokacin da aka dauki hotunan Kanu da ake ta yadawa cewa ya bayyana a kasar Isra'ila.
Shi dai Nnamdi Kanu a watannin baya an dena jin duriyar sa tun bayan da jami'an tsaron Najeriya suka kutsa har cikin gidan sa lokacin da yake ta fafutukar ganin an raba Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng