Wani babban Sarki a Najeriya ya bayyana ma Duniya sabuwar Amaryarsa

Wani babban Sarki a Najeriya ya bayyana ma Duniya sabuwar Amaryarsa

Guda daga cikin manyan Sarakunan Najeriya, kuma shugaban Sarakunan kafatanin kasar yarbawa gaba daya kwata ‘Oni Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi Akande’ dake jahar Osun ya bayyana ma duniya sabuwar amaryarsa a ranar Juma’a 19 ga watan Oktoba, mai suna Sarauniya Morenike Naomi Oluwaseyi.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa shekarun Sarauniya Morenike ashirin da biyar, kuma itace shugaban cocin En-Heralds, cocin da ta kirkira da kanta tun a shekarar 2011 a garin Akure na jahar Ondo.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Kasar Amurka ta kulla yarjejeniyar dala miliyan 10 da jahar Kebbi don inganta noma

Wani babban Sarki a Najeriya ya bayyana ma Duniya sabuwar Amaryarsa
Amarya
Asali: Facebook

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne a shafukansa na kafafen sadarwar zamani, inda ya yabi amarya Morenike, tare da jinjina ma kyawun surarta, da kuma sarautarta, amma abinda yafi so a tare da ita shine riko da addininta.

“Na dade ina jira tare da hakurin Allah ya kawo min mata, sai yanzu Allah ya bani mata, itace Shilekunola, Moronke, Naomi, babbar makamin da zaka rike akan wannan babban kujerar sarauta da nake kai, wanda babban abinda ta kunsa shine ‘Tsoron Allah’. Ina miki maraba da zuwa gidana.” Inji shi.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne basaraken ya salami tsohuwar matarsa, Sarauniya Zainab Otiti-Obanor, wanda gaba daya basu wuce watanni goma sha bakwai da yin auren ba, kamar yadda ta bayyana mutuwar auren a shafinta na Instagram.

Wani babban Sarki a Najeriya ya bayyana ma Duniya sabuwar Amaryarsa
Amarya
Asali: Twitter

“Ina tabbatar da cew daga yau aurena da Oni ya zo karshe, ya nuna min soyayya, kuma ina godiya, zan cigaba da aikace aikace na taimaka ma mata da ake ci ma zarafi ta hanya gidauniyata.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel