Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wata Uwa da 'Ya'yanta 4 a jihar Neja

Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wata Uwa da 'Ya'yanta 4 a jihar Neja

Mun samu rahoton cewa wata Mata, Asma'u Shehu da 'ya'yanta 4, Yusuf, Umma, Hadi da kuma Rabi'at sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyar aukuwar wani mummunan tsautsayi na wutar lantarki cikin unguwar Sarkin Hausawa dake karamar hukumar Bosso a jihar Neja.

Ibrahim Hussaini, kakakin hukumar NEMA mai bayar da agajin gaggawa reshen jihar Neja, shine ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan lamari mai ban tausayi yayin ganawa da manema labari cikin birnin Minna a ranar Larabar da ta gabata.

Mista Hussaini ya bayyana cewa, Asma'u da yaran ta 3 sun riga mu gidan gaskiya nan take yayin tsautsayin na wutar lantarki da ya auku, inda daga bisani na karshe ya ce ga garinku nan a babban Asibitin garin Minna.

Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wata Uwa da 'Ya'yanta 4 a jihar Neja
Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wata Uwa da 'Ya'yanta 4 a jihar Neja
Asali: UGC

Kazalika sauran 'ya'yaye biyu na Marigayiya Asma'u, Hassana da kuma Maryam, na ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a babban asibitin sakamakon karar kwana da ba ta cimma su ba sai dai munanan raunuka da suka samu yayin wannan tsautsayi.

KARANTA KUMA:

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito daga kamfanin dillancin labarai na Najeriya, tuni an yi jana'izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya inda muke rokon Mai Duka ya jikan su.

Jaridar LEGIT.ng ta kuma ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne makamancin wannan tsautsayi na wutar lantarki ya auku can jihar Cross River kan wani dalibin makarantar sakandire dan shekara 12 a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel