Farawa da iyawa: Cacar baki da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin yan takarar shugaban kasa

Farawa da iyawa: Cacar baki da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin yan takarar shugaban kasa

Wasu matasa biyu dake takarar shugaban kasa sun shiga nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki a yayin da cacar baki ta kaure tsakaninsu akan wanda yafi iya tafiyar da mulki a tsakaninsu, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mawallafin kamfanin Sahara Reporters, Omoyele Sowore dake takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar ‘African Action Congress AAC’ ne ya zargi dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyar Young Progressive Party –YYP, Farfesa Kingsley Moghalu akan rashin iya mulki.

KU KARANTA: Wani babban jami’in gwamnati kuma na hannun daman Buhari ya rasu

Sowore ya zargi Moghalu ne da cewa bashi da masaniya game da matsalolin ma’aikata, a cewar Sowore har yanzu Moghalu bashi da wani tabbatacce kuma sahihin tsari na yadda zai kaddamar da karancin albashi ga ma’aikata.

Farawa da iyawa: Cacar baki da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin yan takarar shugaban kasa
Omoyele da Moghalu
Asali: UGC

Sowore ya bayyana haka ne a wata muhawara da suka tafka da juna a gidan talabijin na TVC a ranar Juma’a 12 ga watan Okoba, inda yace Moghalu ya yi watsi da manufarsa na biyan karancin albashi na naira dubu dari dari.

A tattunawar tasu, Moghalu ya kalubalanci Sowore akan me zai biya naira dubu dari dari, inda yace wannan abu ne dake bukatar lissafi da bincike ba wai kawai za ka yi bane don jama’a su yabeka; “Tabbas N18,000 a matsayin karancin albashi shirme ne, ya kamata a kara, amma bai kamata mu zama yan abi yarima a sha kida ba.

“Ba zance ba zan biya N100,000 a matsayin karancin albashi ba, amma abu ne dake bukatar bincike mai zurfi don na samu damar yanke shawara a ilimance, amma ba zan iya kayyade abinda zan iya biya, har sai na gudanar da bincike.” Inji shi.

Sai dai da yake mayar da martani, Sowore ya bayyana mamakinsa da yadda dan takarar shugaban kasa wanda yake ikirarin aiki a bankin duniya bai kammala bincikensa ba akan karancin albashi a lokacin da zabe ya rage saura kwanaki 128.

“Idan har bai kammala bincikensa akan nawa karancin albashi ya kamata ya zama ba a yau da zabe ya rage saura kwanaki 128 ba, tabbas Kingsley bai cancanci zama shugaban kasar Najeriya ba, mu kam mun yi namu binciken, yana can a shafukan yanar gizo, amma gaskiya ina mamakin yadda Kingsley bai san bukatar ma’aikata ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel