Tirkashi: El-Rufa’I ya lissafa sharudan yafewa Shehu Sani

Tirkashi: El-Rufa’I ya lissafa sharudan yafewa Shehu Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya tofa albarkacin bakinsa, a karo na farko, bayan sanatan Kaduna ta tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya yanke shawarar cigaba da zama a jam’iyyar APC.

Sanata Sani ya bawa mutane mamaki da wannan shawara da ya yanke bayan an yi tsammanin zai fice daga APC saboda rashin jituwa tsakaninsa da gwamna El-Rufa’i.

Sanatan na daga cikin Sanatocin jam’iyyar APC 42 a cikin jimillar su 53 da suka kaiwa shugaba Buhari ziyarar nuna goyon baya da jaddada biyayyarsu gare shi.

Tirkashi: El-Rufa’I ya lissafa sharudan yafewa Shehu Sani

El-Rufa’I da Shehu Sani

Da yake amsa tambayoyi yayin wani shirin kai tsaye a gidajen radiyon dake Kaduna a jiya, Alhamis, El-Rufa’i, ya bayyana Shehu Sani a matsayin wanda ya yi riddar siyasa tare da bayyana cewar ba za a karbe shi a matsayin cikakken da APC na halak ba sai ya tuba ya amsa zunuban da ya aikata. Kazalika, El-Rufa’I ya bayyana cewar har yanzu ba a janye dakatarwar da aka yiwa Sanata Sani a mazabarsa ba.

DUBA WANNAN: Sheik Pantami ya bude wani muhimmin aiki da hukumarsa ta yiwa Katsinawa

Sai ya tuba, sannan ya fadawa mutanen jihar Kaduna dalilin da yasa ya cutar da su. Dole kuma ya koma mazabarsa domin har yanzu yana nan a matsayin dan jam’iyya da aka dakatar,” a cewar El-Rufa’i.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin ko gwamna El-Rufa’i zai karbi Sanata Sani tare da yin tafiya tare idan uwar jam’iyya ta kasa ta shiga maganar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel