Mahakurci mawadaci: Buhari ya nada Naja’atu Muhammad wani muhimmin mukami
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohuwar yar gwagwarmaya, Hajiya Naja’atu Muhammad mukamin mamba a hukumar gudanawa ta hukumar Yansandan Najeriya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya yi wannan nadi ne fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli, inda ya kaddamar da hukumar gudanarwar tare da yayanta.
KU KARANTA: Karyar banza: Amurka ta soki kasashen Musulmai kan rashin tallafa ma Falasdinu
Tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, Alhaji Musiliu Smith ne aka nada shugaban wannan hukumar, sai kuma Najatu Mohammed a matsayin wakiliyar Arewa maso yamma, Braimoh Austin kudu maso kudu, da Rommy Mom Arewa ta tsakiya.
Sauran mambobin wannan hukuma sun hada da Nkemka Jombo-Ofo wakilin Kudu maso gabas, Clara Ogunbiyi wakiliyar kudu maso yamma da AIG Lawal Bawa a matsayin wakilin Arewa maso gabas.
Ita dai Naja’atu ta kasance tsohuwar shahararriyar mai goyon bayan shugaban kasa Buhari tun daga shekarar 2003 zuwa 2007 da ya tsaya takara, amma a shekarar 2011 bata yi Buhari ba, sai ta kafa tanti da Nuhu Ribadu dan takarar jam’iyyar ACN, har sai a 2015, inda suka dinke barakar dake tsakaninsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng