Wani Sanata ya nemi a tsige Gwamnan Zamfara Yari daga ofis

Wani Sanata ya nemi a tsige Gwamnan Zamfara Yari daga ofis

Mun samu labari cewa wani ‘Dan Majalisar Dattawa da ke wakiltar Zamfara ta tsakiya ya nemi a tsige Gwamnan Jihar Abdulaziz Yari saboda kashe-kashen da ake cigaba da yi a Jihar har gobe.

Wani Sanata ya nemi a tsige Gwamnan Zamfara Yari daga ofis

Maganar tsige Gwamnan Zamfara daga kan kujerar sa na karfi

Sanata Saidu Dansadau wanda ke wakiltar Jihar Zamfara a Majalisa yayi kira a tsige Mai Girma Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar saboda rashin yin aikin sa na tsare rayukan al’ummar Zamfara a matsayin sa na Gwamna mai iko.

Saidu Dansadau yace ikirarin da Gwamnan yayi na cewa harkar tsaron Jihar ba ta hannun sa ta sa ya zama dole a kafa dokar ta-baci a Jihar. Sanatan ya nemi Shugaban kasa yayi amfani da ikon sa ya kafa dokar ta-baci a Jihar Zamfara.

KU KARANTA: Wani ‘Dan Majalisa ya nemi Buhari ya sauka daga mulki saboda kashe-kashe

Sanatan kasar ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi amfani da wasu bangare na sashe na 305 na dokar kasa ya kuma nada wani Shugaban rikon kwarya a Jihar Zamfara har zuwa lokacin da sha’anin tsaro ya dawo daidai a Jihar.

‘Dan Majalisar yace idan har ba a dauki mataki ba, dajin na Zamfara wanda ya hade da Yankin Katsina, Kaduna, da Neja da ma irin su Jihar Kebbi zai zama matattarar ‘Yan ta’adda kamar yadda Dajin Sambisa ya zama ana ji ana gani a kasar nan.

Dansadau yace sun gama shirin tsige Gwamnan tuni saboda sakacin sa inda ya yabawa kokarin Gwamnonin da ke makwabtaka da Zamfara na kawo zaman lafiya. Dazu dai kun ji an nemi Buhari ya ajiye mulki saboda sha’anin tsaron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel