Majalisa ta sake gayyatar IG Idris a kan kisan 'yan sanda 7 a Abuja

Majalisa ta sake gayyatar IG Idris a kan kisan 'yan sanda 7 a Abuja

Kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yan sanda ta gayyaci Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bayyana a gabanta don yin bayyani game da kisar gillar da aka yiwa wasu yan sanda bakwai a ranar Litinin a Abuja.

Ciyaman din kwamitin, Abu Ibrahim na jam'iyyar APC mai wakiltan Katsina ta Kudu ne ya bayar da sanarwan a ranar Alhamis bayan shugaban majalisar Bukola Saraki ya bayar da umurnin cewa a gudanar da bincike game da batun.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun samu gawar 'yan ta'addan Zamfara 41 da aka kashe

Mr Saraki ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar yan sandan a yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a kan batun yawaitar shingen yan sanda da sojoji masu dauke da makamai a titunan Kudu maso gabashin kasar da Sanata Mao Ohabunwa ya gabatar.

Majalisa ta sake gayyatar IG Idris a kan kisan 'yan sanda 7 a Abuja
Majalisa ta sake gayyatar IG Idris a kan kisan 'yan sanda 7 a Abuja

Ya janyo hankalin sauran Sanatocin bisa rasuwar jami'an yan sandan wanda ya ce sun mutu ne yayin da suke yiwa kasarsu hidima.

"A matsayinmu na majalisa, ya kamata mu mayar da hankali kan yadda jami'an tsaro ke rasa rayyukansu kamar yadda muke daukan mataki kan kashe farin hula. Suma masu kare mu ya kamata akwai masu kulawa dasu.

"Ina son mu gano abinda ya faru da yan sanda bakwai da suka rasu da kuma yadda zamu taimakawa iyalensu saboda dukkansu su san cewa mun damu da abubuwan dake faruwa dasu. Ya kamata mu samu rahoto cikin mako mai zuwa," inji shi.

Mr Ibrahim kuma ya sanar da majalisar cewa Sifeta Janar na yan sanda zai bayyana don yi musu bayyani ranar Talata.

Mr Saraki kuma ya bukaci kwamitin ta sanar da majalisa sakamakon ganawarsu da Sifeta Janar din cikin mako mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel