Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tawagar majalisar Dinkin Duniya (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi tawagar majalisar Dinkin Duniya a fadarsa dake Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Yuni.
Tawagar sun kawo masa ziyarar ban girma ne karkashin jagorancin babban sakataren majalisar dinkin duniya Mista Zurab Pololikashvili.
Tare da shugaban kasar akwai Ministan bayanai da al’adu Alhaji Lai Mohammed, shugaban ma’aikata, Mallam Abba Kyari da kuma babban darakta na kungiyar bude ido na duniya Zhu Shanzhong.
Ga hotunan a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng