Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne jaruma Hauwa Maina
An sada jarumar shirya fina-finan Hausa Hauwa Maina da gidanta na gaskiya.
Anyi jana’izar jarumar ne a jihar Kaduna, a yau Alhamis, 3 ga watan Mayu.
Shafin Kannywood ta wallafa hotunan jana'izar jarumar.
Kamar yadda muka kawo a baya, marigayiya Hauwa ta rasu ne a wani asibiti dake jihar Kano.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Barayin shanu sun kai hari a wani kauyen Zamfara sun kashe mutane 13
Ta rasu ne a daren ranar Laraba, 2 ga watan Mayu bayan tayi fama da jinya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng