Matsalar shaye shaye a tsakanin matasan Arewa: Kulalliyar shiri ne na Inyamurai – Inji wani Malami

Matsalar shaye shaye a tsakanin matasan Arewa: Kulalliyar shiri ne na Inyamurai – Inji wani Malami

Wani Malamin jami’ar, Dakta Bala Muhammad, kuma tsohon shugaban hukumar A daidata sahu na jihar Kano, ya bayyana cewar matsalar shaye shaye a Arewa wata kitimurmura ce Inyamurai ke shirya ma Arewa.

Daily Nigerian ta ruwaito Bala na cewa hadin bakin manyan yan kasuwan Inyamurai ne da wasu yan kasuwan Arewa ne don lalata rayuwar matasan yankin, ya bayyana haka ne a cikin wata kasida da ya gabatar a yayin wani taron matasan jihar Kano a ranar Litinin.

kKU KARANTA: Yansanda sun cafke yan sara suka 23 da suka kashe wani tare da kona gidaje a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bala na mamakin yadda Kodin bata yawaita a kasashen Inyamurai ba, sai a Arewa? Don haka yace musamman ake hada maganin tari mai dauke da Kodin don kaiwa Arewacin Najeriya saboda matasan yankin.

“Bincikenmu ya nuna cewar shaye shaye yafi karfin Kodin, giya ko wiwi, har ta kai ga magungunan da muke sha don magance cututtuka ma an mayar da su kayan shaye shaye, mun gano hannun Inyamurai da wasu bata gari a Arewa wajen kawo Kodin zuwa yankinmu.

“Mun sha kama Inyamurai suna safarar Kodin a jihohin Arewa, amma me yasa basa kaiwa jihohinsu? Wannan ya zama dole mu tashi haikan wajen magance matsalar.” Inji shi

Haka zalika Malamin jami’an ya zargi Alkalan kotuna da bada belin mutanend aaka kama da safarar miyagun kwayoyi, ba tare da yanke musu hukunci ba, daga nan ya shawarci jama’a da su daina nuna ma yan shaye shaye wariya, ta hanyar janyo su a jikine kawai za’a yi maganin matsalar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: