Da dumi-dumi: T.Y Danjuma ya sha da kyar a hannun matasan Taraba

Da dumi-dumi: T.Y Danjuma ya sha da kyar a hannun matasan Taraba

Matasan jihar Taraba sun far ma tsohon ministan tsaron Najeriya, Janar Theophilis Danjuma, bayan ya yi jawabin cewa mutane su dau makami su kare kansu daga makasa.

Wannan magana da yayi ya tada jijiyoyin wuya a fadi tarayya yayinda wasu masu sharhi suka siffanta shi a matsayin magana da ka iya raba kan yan Najeriya.

Matasan sun yi ta kan Janar TY Danjuma ne da yammacin Jiya Litinin, 26 ga watan Maris 2018 a garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Da dumi-dumi: T.Y Danjuma ya sha da kyar a hannun matasan Taraba
Da dumi-dumi: T.Y Danjuma ya sha da kyar a hannun matasan Taraba

Matasan sun yi masa iwu barawo har jami'an tsaronsa suka fara harbe-harben bindiga domin tarwatsa mutane.

KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kasar Switzerland kan dawo da kudaden Najeriya

Janar T.Y Danjuma tsohon soja ne kuma tsohon ministan tsaro karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng