Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun yarje a rage farashin lantarki na watanni 3

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun yarje a rage farashin lantarki na watanni 3

- Daga karshe, gwamnati da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya

- Da alamun an ajiye maganar yajin aiki gefe har sai bayan watanni uku masu zuwa

- Gwamnati ta umurci kamfanonin wutan lantarki su rage farashin wuta da kwastomomi zuwa karshen shekara

Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun yi yarjejeniyar amfani da harajin VAT wajen bada tallafin wutan lantarki ga yan Najeriya na tsawon watanni uku masu zuwa.

An yanke shawaran haka ne ranar Litinin a Abuja bayan zaman kwamitin yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon NLC da na TUC.

An fara zaman ne tun ranar Lahadi karkashin jagorancin karamin ministan kwadago, Festus Keyamo.

Daga cikin abubuwan da aka yanke shine a yiwa wasu kwastamomi rahusan N10.20/kWh na tsawon watanni uku, sannan a rabawa yan Najeriya na'urar mita milyan shida bayan karewar wa'adin makonni biyun da aka bada a watan Satumba.

Hakazalika an yarje cewa an samar da albashi mai kyau ga ma'aikatan kamfanonin lantarki, a mayarwa mutanen da aka cirewa kudin fiye da yadda ya kamata, sannan kuma hukumar lura da wutan lantarki NERC ta rika wallafa kudin da marasa mita zasu rika biya kowani wata.

Wadannan shawarwari da aka yanke na kunshe cikin jawabin da Mista Keyamo ya saki ranar Litinin a shafinsa na Tuwita, @fkeyamo.

Za ku tuna cewa a watan Satumba, NLC da TUC sun yi barazanar tafiya yajin aiki idan gwamnati bata janye karin kudin wutan lantarki da man fetur ba.

Ana saura yan mintuna a fara yajin aka cimma matsaya.

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun yarje a rage farashin lantarki na watanni 3
Karamin ministan kwadago Credit: Pulse.ng
Asali: UGC

A bangare guda, Cibiyar CHRICED da ke kare hakkin bil Adama ta yi watsi da uzurorin da kungiyoyin NLC da TUC su ka bada na janye yajin-aikin da su ka shirya a da.

Babban darektan cibiyar, Dr. Ibrahim Zikirullahi ya maida martani a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020, bayan kungiyoyin sun fasa yin yajin.

Ibrahim Zikirullahi ya ce ba su goyi-bayan tafiya yajin-aikin da wasa ba, domin kuwa zuwa yajin zai taimaka wajen sa gwamnati ta dawo cikin taitayinta.

KARANTA WANNAN: Ba zamu yarda ba, sai ka janye - Sanatocin PDP kan nadin hadimar Buhari matsayin kwamishana a INEC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel