Koriya ta Arewa ta ba da gudummawar taimaka wa Najeriya akan yaki da Boko Haram

Koriya ta Arewa ta ba da gudummawar taimaka wa Najeriya akan yaki da Boko Haram

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kasar Koriya ta Arewa ta yiwa Najeriya sabon albishir, na gudummawar taimakon dakarun sojin kasar wajen fafutikar su ta ganin karshen ta'addancin Boko Haram da ya yi kamari a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Babban jakadan kasar mai murabus, Mista Jong Yong Chol, shine ya bayyana hakan a yayin ziyarar bankwana da ya kaiwa Ministan harkokin kasashen na Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama, inda ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar kan kokarin ta na yakar ta'addanci.

Shugaban Koriya ta Arewa; Kim Jong-Un
Shugaban Koriya ta Arewa; Kim Jong-Un

Da yake cewa, a matsayin sa na wakilin kasar Koriya ta Arewa, yana mika sakon taya murna dangane da irin nasarorin da Najeriya ta samu wajen yaki da ta'addanci na Boko Haram.

Ya kuma bayyana albishir din sa ga gwamnatin Najeriya da cewar kasar sa za ta bayar da gudummuwar taimakon dakarun sojin kasar nan wajen kawo karshen ta'addanci.

KARANTA KUMA: Nau'ikan abinci 7 mafi shahara a al'adun Najeriya

Jakadan ya kuma mika godiyar sa ga gwamnatin Najeriya dangane da dankon zumunta da kuma kulalliyar abota dake tsakanin kasashen biyu tun a shekarar 1976 wajen habakar tattalin arziki, siyasa da kuma al'adu.

Jaridar Independent ta ruwaito cewa, jakadan ya kirayi gwamnatin Najeriya kan bayar da muhimmanci wajen ci gaba da zumuncin dake tsakanin kasashen biyu tare da bayar da tabbacin sa na goyon bayan al'ummar kasar sa wajen aiwatar da hakan.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta cafke wani mahaukaci da laifin kisan dalibai biyu a jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng