Kisan Benuwe: Abubuwa 10 da gwamna Ortom ya fada wa Buhari yayin ziyarar sa

Kisan Benuwe: Abubuwa 10 da gwamna Ortom ya fada wa Buhari yayin ziyarar sa

A ranar Litinin, gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, yayi maraba da shugaba Muhammadu Buhari, a ziyararsa ta farko daya kai jihar ta Binuwai tun hawansa mulki a shekarar 2015.

Buhari ya jajantawa al'ummar jihar bisa rasuwan mutane da kuma asarar dukiyoyi sakamakon rikice-rikicen da ya barke a jihar, a jawabinsa gwamna Ortom ya yi bayyanai kan rikicin na makiyaya da manoma a jihar.

1) A ranar 11 ga watan Janairu, mun binne mutane 73, wadanda suka hada da maza da mata. Dukkansu ‘yan ta’adda ne suka kashesu suna cikin bacci a sa’o’in farko na shakarar 2018. Bayan haka a kalla mutane 65 aka kara kashewa a kananan hukumomin Guma da Logo bayan janazar taro. Kwanaki kadan da suka wuce mutane 26, maza da mata da kuma yara a kauyen Okpokwu aka kashe. Bayan haka, mutane 5,000 ne suka bar gidajensu a Mbatoho karamar hukumar Makurdi.

2) Makiyaya sun cigaba da kai hari akauyukan jihar, wanda ya sanya mutane 170,000 sun gudu daga gidajensu. Kashi 65 daga cikinsu yarane wadanda dole tasa sun bar makaranta. Wadannan da ma wasu da dama suna zama asansanin ‘yan gudun hijira guda takwas a ko ina na fadin jihar, irinsu; Abagana, Daudu 1 and 2, Gbajimba, Tseginde,Anyiin, Abeda, da kuma Ugba. Gidajensu da gonakinsu duk ‘yan ta’addan Makiyaya sun lalata.

KU KARANTA: Da dumimsa: Bayan fiye da shekara guda, Majalisa ta yafe wa Abdulmumin Jibrin

3) Muna godiya ga shugaban kasa, da kawo mana daukin gaggawa bayan hare-hare. Ka gaggauta turo mana Kwamandan ‘Yan Sanda na kasa zuwa Binuwai don tsayar da kashe-kashen da akeyi. A sakamakon haka kungiyar bada agajin gaggawa ta NEMA ta bada tallafin kayayyaki ga sansanin ‘yan gudun hijira duk da dai ba magance matsalar bane. Suna godiya a gareka sakamakon tura jami’an tsaro na ‘yan Sanda da Civil Defence da akayi garuruwan nasu wanda yasa an samu ragowar hare-hare duk da dai suma sunji jiki a kokarin kawo zaman lafiyan da sukayi.

4) Mai girma shugaban kasa, muna rokonka da ka dauki mataki wajen rage wahalhwalu na sama da mutane 170,000 na mutanen kasar nan na sansanin ‘yan gudun hijira takwas da muke dasu a jihar. Gwamnatin tarayya ta tallafa masu da agaji na sake gina masu Gidaje kamar yanda kwamitin masu kula da ‘yan gudun hijira wanda mataimakin shugaban kasa ke jagoranta suka alkawalta. Makarantun Primary da Secondary, da Coci da wuraren kula da lafiya da aka lalata masu a kananan hukumomi.

5) Duk da hare-haren a kauyukan sun fara ne tun shekarar 2011, tsakanin 2013-2017, an samu hare-hare arba’in da bakwai, kuma sama da mutane 1,878, aka kashe maza, mata da yara, a kananan hukumomi 14 a jihar. An raunata wasu 750, sai wasu 200 kuma sun bace, sama da gidaje 99,427 abun ya shafa. Mun rasa kashi 47 na haraji da muke samu sakamakon harin da Makiyaya ke kaiwa a jihar. Wannan ya jamyo matsalolin Makiyaya da Manoma.

6) Bayanan tsaro da da aka gabatar a gaban Shugaban kasa, jihar Musulunci a Jihar yammancin Afrika ISWA suna da hannu a kisan da akeyi a jihar Binuwai. Idan bayanai a kan Binuwai gaskia gaskia ne, suna da tasiri da barazana ga tsaron Najeriya. Akwai bukatar a kara tsaurara tsaro a na ka’idojin kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Africa na Yamma ECOWAS.

7) A ranar 30 ga watan Mayu, shekarar 2017, kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre a wani taro da akayi a Abuja, sun juya baya ga dokar wurin kiwo. Sunyi kira ga Filanin dake Yammacin Afrika dasuzo su taimaka masu wurin karbar kasarsu. Kungiyar ta Miyatti Allah a wani bayanin gaggawa da sukayi su bayyana cewa za’a cikigaba da zubar da jini idan ba’a janye dokar kiwo ba. Mai girma shugaban kasa mua masu goyon bayan doka, mai girma shugaban kasa muna rokon daka bada izinin gaggauta kamowa da hukunta shugabannin Miyetti Allah Kautal Horre da kungiyar masu Shanu ta Miyetti Allah na wannan harin da ake kawowa a jihar Binuwai, akan dokar kiwo a ko ina ta shekarar 2017.

8) Alokacin da aka rantsar dani a watan Mayu, shekarar 2015, abu na farko da gwamnatinmu ta farayi shine afuwa ga matasan da ke daukar makamai suna barazana ga tsaro a jihar. Anyi taron afuwa a fili inda aka maido da makamai 700 da harsasai da dama. Kwamitin shugaban kasa na kananan kungiyoyin masu rike makamai da kungiyar haka MAG, ta kasar Sawus Afrika da su kula da makamai da aka karba daga hannun mutane sama da 900 karkashin aikin kungiyar.

9) Ta hanyar dubawa da bincike, mun gano cewa hanya mafi inganci ta kula da dabbobi itace ta hanyar kiblacesu. Kasashen dake jagoranci wurin san’ar shanu kamar su Indiya, Brazil, Amruka, Sawus Afrika, Kenya da kuma Zibabuwe, sunyi suna da kiwon gidan gona. Hakan yana inganta lafiyar dabbobi da kuma nama da kayan gona. Wannan itace dabarar yin wurin kiwo a wanda ya samu goyon bayan dokar hana kiwo a ko’ina ta shekarar 2017, mai girma shugaban kasa, duk kuma wanda yake da wata dabara banda wannan to ya kawota a teburi domin a duba. Dokar da Majalissar jihar ta kaddamar wanda shine muradin ‘yan jihar ta Binuwai.

10) Mai girma shugaban kasa, maza da mata, wannan ba lokaci bane na bayyana manya-manyan abubuwan ci gaba da muka samu a bangaren Ilimi, inda sama da Makarantu 711 aka gyara sai Malamai 16,000 da aka horar. Ya kamata mu sake duba bangaren kiwon lafiya inda makarantun da aka rufe na Nursing da Midwifery data Health Technology Agasha an gyarasu, an kuma budesu, sun kuma samu amincewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164