APC ta gode ma Tinubu kan amsa tayin shugaba Buhari da yayi
- Jamíyyar APC ta yaba ma Tinubu bisa amsa tayin da shugaba Buhari yayi masa
- Ta jadadda cewa shi yafi cancanta da wannan matsayi duba ga kwarewarsa a harkar siyasa
- Ta kuma yaba ma shugaba Buhari kan kokarinsa na son ganin ci gaban jam’iyyar
Jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta nuna godiya ga Asiwaju Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar ta kasa kan amsa nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi masa a matsayin uban sulhu na jam’iyyar.
Da yake Magana da jaridar Independent, Mallam Bolaji Abdullahi kakakin jam’iyyar wanda ya bayyana yunkurin a matsayin ci gaba mai kyau yace irin wannan matsayi na bukatar mutun da ya kware a harkar siyasa sannan kuma suna ganin Tinubu ya hada dukannin abubuwan da ake bukata.
KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Fim ya fi aikin soja wahala – Inji Rabi'u Rikadawa
Jam’iyyar ta kuma yaba ma shugaba Buhari da ya bayar da muhimmanci ga ci gaba tare da hadin kan jam’iyyar da kuma ganin cewa wannan matsayi ya dace da Tinubu.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa cikin shirin kokarin inganta hadin kai cikin jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya jagoranci shawarwari, sasantawa da gina amana a jam’iyyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng