Kotu ta ba ‘Yan Sanda gaskiya a wajen shari’a ta da Evans ne ci masa mutunci

Kotu ta ba ‘Yan Sanda gaskiya a wajen shari’a ta da Evans ne ci masa mutunci

- Evans da ake zargi da garkuwa da mutane ya kai karar Shugaban ‘Yan Sanda

- Evans ya nemi ‘Yan Sandan su biya shi Miliyoyin kudi na ci masa mutuncin sa

- Kotu tayi watsi da karar na Evans tace babu abin da aka yi masa na saba doka

Evans ya nemi Kotu ta ba ‘Yan Sanda umarni su bada belin sa ko kuma su maka sa a Kotu. Haka kuma wanda ake zargin ya nemi a biya sa kudi har Naira Miliyan 300 saboda keta masa alfarma da aka yi a tsare kafin a kai shi gaban Alkali.

Kotu ta ba ‘Yan Sanda gaskiya a wajen shari’a ta da Evans ne ci masa mutunci

Evans yana karar 'Yan Sanda da keta masa mutunci

Alkali mai shari’a Abdulazeez Anka yayi watsi da wannan kara da Evans ya kai a babban Kotun Tarayya da ke Legas. An yi wannan zaman ne a jiya kamar yadda labari ya zo mana. Evans kuma ya nemi a daina yawo da shari’ar ta sa a wajen Kotu.

KU KARANTA: An bada belin Kwamishinan da yace a jefi tsohon Gwamna

Olukayode Ogungbeje wanda shi ne Lauyan da ke kare Evans yana zargin ‘Yan Sanda da rike sa fiye da kima a dokar kasa. Alkali mai shari’ar dai yace Jami’an ‘Yan Sanda ba su saba doka ba muddin ba a zarce kwanaki 90 ana rike mai laifi ba.

Bayan haka Alkali yace ba zai hana masu aikin Jarida yin aikin su ba kamar yadda shi Evans yake gani ba ayi masa adalci ana yama-didi da shari’ar ta sa a gaban Duniya. An dai nemi wanda bai gamsu da hukuncin ba ya daukaka kara a Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel