Ta yi ma wani kato duka yayin da yayi kokarin cire mata Hijabi (Hoto/bidiyo)
1 - tsawon mintuna
Wani bidiyon ya yawaita a shafukan yanar gizo wanda a cikin sa wata budurwa musulma take dambe da wani kato a kusa da ajinsu a makaranta.
Kamar yadda wata yar jarida yar kasar Somalia mai suna @Daudoo ta bayyana, tace budurwar tayi biji biji da mutumin ne a lokacin da yayi kokarin cire mata Hijabi.
KU KARANTA:Abin mamaki: Akuya da kwankwadar lemun kwalba (Bidiyo)
Daudo tace “kada wani ya kuskura ya raina yan matan Somalia, abinda ya ja ma wannan saurayi cin duka kenan yayin da yayi kokarin cire mata Hijab a makaranta dake garin Minnesota kasar Amurka.”
Ga bidiyon fadan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng