An jefar da wani kyakkyawan jariri a cikin kungurmin daji (Hotuna)
- Allah yayi ma wani jariri tsawon rai a jihar Legas
- Matasa ne suka tsinci jaririn a wani dajin jihar
Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana mazuru ana shaho sai yayi, wannan shine gaskiyar abinda ya auku da wani jariri da aka zubar da shi a wani daji, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.
Wannan jariri yayi tsawon rai ne yayin da wasu yan kasa nagari suka tsince shi a kusa da unguwar Ikorodu na jihar Legas.
KU KARANTA: Jama’a sun hana Buhari shiga mota a Daura, yayi tattaki zuwa gida da ƙafansa (Hotuna)
Jama’an sun jiyo kukan jaririn ne a da safiyar ranar Laraba 30 ga watan Agusta, inda sakamakon halin da suka tsince shi a ciki, har wanka suka yi masa, sa’annan suka sanya masa kaya, kamar yadda hotunansasuka nuna.
Ana yawan samun rahotannin satar jarirai da kuma jefar da jarirai a kan titunan daban daban na sassan kasar nan, wannan kuwa na faruwa sakamakon yawan samun cikin shege daya yawaita a tsakanin al’umman kasar nan.
Ga bidiyon nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng