Shia: Gwamnati ta haramta tattaki

Shia: Gwamnati ta haramta tattaki

– Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta tattaki a fadin Jihar

– Gwamnati tace daga yanzu babu wani taro na gaira-babu dalili

– Ana hakan ne domin a kawo karshen ‘Yan kungiyar IMN na Shi’a a Jihar

Shia: Gwamnati ta haramta tattaki
Shia: Gwamnati ta haramta tattaki

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa daga yanzu babu wani tattaki ko gangamin da ya sabawa doka a Jihar. Gwamnatin tayi wannan ne domin kawo karshen lamarin ‘Yan Kungiyar IMN na Shi’a a Yankin.

Mai magana da bakin Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a jiya. Bayan wani taro da Jami’an tsaro na Jihar, Gwamnan ya dauki wannan mataki na dakatar da ‘Yan Kungiyar har tsawon wani lokaci.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram

Kafin yau dama can Hukumar ‘yan sanda sun gargadi ‘yan kungiyar. Bayan nan ne gwamnati ta saka kungiyar cikin ‘yan tawaye, wanda kungiyar tace ba za ta yarda ba. Takardar da aka fitar jiya ta bayyana cewa ‘Yan Kungiyar IMN din ‘yan tawaye ne masu tada zaune-tsaye don haka dole a dauki mataki game da su da Shugaban su da ke tsare, Ibrahim Zakzaky.

Gwamnan yace anyi hakan ne domin kawo zaman lafiya a Jihar. Gwamnan yace zai Hukunta duk wanda ya saba wannan doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng