‘Yan Zaria sai murna suke yi an fatattaki makarantar Shi’a
- Mabiya Kungyar IMN ta shi’a sun saba fito-na-fito da Hukuma a Kasar nan
- Don haka Gwamnati ta haramta ayyukan ‘yan shi’a a Jihar Kaduna
- Ana tunanin Kungiyar na da goyon baya daga kasashen ketare
Jama’a sun shiga tsalle suna murna a Garin Zaria bayan da aka rusa wata Makaranta ta Kungiyar IMN ta ‘Yan shi’a. Hukuma dai ta rusa Makarantun na Firamare da Sakandare na shi’a ne a Jiya, Alhamis.
An rusa wannan Makaranta mai suna Fudiyya da ke Babban Dodo da ke Gangaren Fadama cikin Zaria City. Gwamnatin Jihar ce dai ta bada umarni rusa wannan cibiyar Makaranta. Wannan makaranta Fudiyya ta mabiya shi’a ce.
KU KARANTA: ISIS sun kai harin bakin wake
A kwanakin baya Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya haramta ayyukan shi’a a fadin Jihar. Gwamnoni da dama kuma suka yi ta bin sahu a fadin Arewacin Kasar. ‘Yan unguwar dai sun yi tsalle da farin ciki da aka ruguza wannan makaranta, wani mazaunin wurin yace madalla, abu yayi daidai.
Shugaban Kungiyar dai ta Islamic Movement of Nigeria (IMN) yana nan a tsare tun shekar bara. Kwanan an kara samun wata takkadama tsakanin ‘Yan Shi’a da ‘Yan Sanda a Garin Kano.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng